Kannywood

Kalli jerin yan kannywood mata da suka fara film tun suna yara da kuma bayanai akansu.

Yawancin jaruman kannywood sai da suka girma suka kai minzalin mallakar hankali sann suka shigo masanaantar kannywood, hakan ba wai yana nufin babu wayanda tun suna yara ake damawa da su a matsanaantar ba.

MARYAM MALIKA

Jarumar da ta koma harkar fim kwanan nan bayan mutuwar auren ta wato maryam malika, tayi suna ne da kuma samun wannan lakabi na malika da ake mata a sanadiyar wani fim da ta fito a ciki mai suna malika, jarumar bayan ta girma ta fara fitowa ne a wani film mai suna wasila 2010 kuma a shekarar 2010 ta fara fitowa a finafinai bayan ta girma kamar yadda ta bayyana.

jarumar akwai wani film da aka ganta ta fito a ciki a lokacin tana yarinya karama tare da marigayiya Balaraba Muhammah da ya haura shekaru 20 wanda shi ya tabbatar da cewa tun tana yarinya karamar take fitowa a finafinai.


 
MARYAM BOOTH


Maryam booth jarumar mai shekaru 28 da aka haifa a garin kano a nigeria, kasantuwarta tun tana yarinya karama mahaifiyarta wato zainab booth take fitowa a finafinan hausa, hakan yasa itama tun tana yarinyar karama ake sanyata a finafinai har ta girma ta kai wannan matsayin da ake kallonta da shi a kannywood a yanzu. jaruma ta fito a finafinai da yawa na kudancin nigeria da kuma na arewacin nigeria wato kannywood. kamar su dijangal, suwaga, gani ga ka.


 
UMMI RAHAB


Jarumar mai tashe a wannan lokacin wacce aka haifa a garin kaduna ranar 7 ga watan april 2003 inda take da shekaru 19 yanzu da haifuwa, jarumi adam a zango shi ya fara sakata a wani film mai suna ummi a lokacin tana yarinya karama, daga baya tabar fitowa a finafinai sai bayan ta girma adam a zango ya sake dauko ta ya saka ta sabon film nashi da ya shirya mai suna fain wata shakallo. wanda har yanzu tana fitowa a wasu finafinan.


 
AMUDE BOOTH


Amude ya kasance kanine ga jaruma maryam booth kuma shima ya kasance ‘da ne ga jaruma zainab booth mai rasuwa shima dai tun yana yaro karami ake ganisa yana fitowa a finafinai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu