Kannywood

Tattaunawa Da Fati Shu’uma Akan Rayuwar Ta Da Baku Sani Ba. Wai Adam A Zango Saurayin kine?

DAME KIKA KARYA YAU ?

Shinkafa da miya da wake.

WANE HALI KIKA SHIGA LOKACIN DA AKE FARGABAR KORONA ?

Nashiga tashin hankali Matuka koda yaushe ina wanke hanu da sanitizer so gaskiya na tsorata.

SHIN A ZAHIRI KE SHU’UMA CE ?

Hmmm, Aa kawaii fim ne ni ba shu’uma bace.

ME YASA KIKE YAWAN FITOWA A SHU’UMA ?

Ehh, to idan kaga ana yawan saka mutum a abu daya to ya iya neh.

saboda ni nafi jindadin wannan ma.

WANE NE SAURAYIN KI NA FARKO ?

Ehh, tin Ina primary school saurayina na farko.

WAYE A KE YAYI YANZU ?

Zaku gani ba sai na fadaba.

AN TABA GULMARKI TA DAWO KUNNEN KI ?

Ehh, sosai ba daya ba biyu bah wannan ta zama kama hanji ga mutane gulma.

KIN TABA DAUKAR MATAKI ?

Eh na taba daukowa wasu mata guda biyu yan sanda.

ME KIKA FI TSANA A DUNIYA ?

Eh na tsani makaryaci da mai Hassada gaskiya.

WADANNE ABUBUWA KUMA KIKA FI SO ?

Ehh, ina son mutum mai bani kulawa da gaskiya da rukon Amana ina son wannan.

ME KIKA YI DA BA ZA KI TABA MANTAWA DA SHI BA ?

Eh akwai wani laifi da muka taba yi a makaranta ta government akan wani malami na Arabic.

Idan time din shigowar sa yayi to sai mutafi can bayan makaranta sanda ya kamamu gaskiya mun daku.

ME KIKE YI YANZU KI JI KE BABBAR YARINYA CE ?

Toh, shine zan hau mota zanje wajan Sana’a ta naci duk abin da nake so.

WANE IRIN ABINCI KIKA FI SO ?

Kamar tuwan shinkafa miyar kubaiwa da man shanu da soyayyen nama.

ME KIKE YI A GIDA DA KE DAUKE MIKI KEWA ?

Ehh, idan bani da aiki ina kira manager na muje gidan gona wajen kaji da kifaye wannan abun yana bani nishaɗi da daukemin kewa.

KE BUDURWAR ZANGO CE ?

Aa, gaskiya ba saurayina bane mai gida nane kawaii.

MENE NE BABBAN BURINKI A RAYUWA ?

Babban burina shine nayi kudi na taimaki mata suyi karatu.

MAGE KO KARE, WANNE KIKA FI SO ?

Ehh, ina tsoransu gaba daya amma nafi tsoran kare amma nafi son kare.

Kasance da *Manuniya.com domin samun sabbin labaran kannywood dan samun nishadin Ku . Saboda jin dadinku shine namu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu