Kannywood

Tattaunawa Baballe Hayatu Akan Rayuwar Sa Da Baku Sani Ba. Ina Da Budurwa Fati

ZAKA SO A DAWO DA BARA BANA ?

Idan har zan so a dawo da bara bana idan har a nayi so zan so a dawo dani lokacin da mahaifana suna raye.

WACE CE BUDURWAR KA TA FARKO ?

Hmm, sunan ta FATI wasu zasuyi dariya Wanda suka sani wasu zasu dauka wace FATI nayi ‘yan mata da yawa masu suna FATI Wanda har abun ya dinga bani tsoro da dariya.

WANE LAIFI KA TABA YI A KA CE A KAMO KA

KA GUDU ?

Akwaii wani lokacin da mukayi jarabawa ta class 3 zamu tafi class 4 a secondary sai naci dawakin tofa danaci dawakin tofa zan tafi makaranta ta kawaji secondary school to sai ya xamana cewa ni dawakin tofa to akwai wani a unguwar mu kusan da area mu kullum muna tare sai muka dan samu matsala.

Sabo da ya girme mu kuma yana da cin zali muka danyi rigima ni kuma na zage shi kawai muna zaune sai a kace wane yaci dawakin tofa sai ya kalleni kuma senior nane a dawakin tofa sai yace wane yaci dawakin tofa yace Abubakar a dawakin tofa sai yace alhamdulillah yace wallahi saina ci ubanka.

yace zaka zo ka same mu wannan maganar yasa gaba daya na tsorata wannan dalilin yasa gaba daya na tsorata a ka dinga guje-guje dani kullum da safe a ka saka kaya za’a kaini gashi an hada kayan makaranta za’a kaini amma idan natuna mugune ko a unguwar mu ansan mugune.

kuma an bani labari na irin muguntar da suke a makaranta wallahi gari yana waye wa ake tsere dani a gida kullum baza’a ganniba sai dare.

WAYE GWANIN KA A KWALLON KAFA ?

Babu ruwa na dasu Sabo da bana kallon boll kuma ina tare da yan boll ina xagaye da yan boll kuma alhamdulillah naci arzikin boll amma ni boll bata dameni bah kuma har yanzu ina subscribe na DSTV sabo da boll amma Bani nake kallo bah abokaina ne suke kallo.

KA TABA YIN FADA A YARINTAR KA DA A KA YI MAKA DUKA ?

Duk Wanda yace baiyi wannan bah kai ko a daji ka taso karyane kace baka tabayin wannan ba amma sai dai mu bawa juna kashi ko ince nafi basu kashi bawai yabon kaiba saboda a lokacin akwai step sister dita koda yaushe muna tare.

Makaranta ta boko ko ta allo to ba yarda za’ayi ka taba daya bakayi fada da mutum biyu bah Zara tana da wani takalmi Wanda take amfani dashi a wajen fada sosai.

bayan mahaifinmu ya rasu mamanta ta dauketa ta tafi da ita garinsu Maiduguri to da muna da Fikon Location dasu sai ya zamanto ba Tunda ba lokaci ne na waya ba Wanda ya zamanto daga lokacin har yanzu da nake maka magana bansan a ina take bah bamu san a ina take bah bamu San ina zamu same ta ba.

Wanda itama daga baya Mahaifiyarta ta rasu Wanda mun tambayi mutane da yawa Wanda mutum na karshe ya fadamin Address din inda za’a same su saina dauka na rubuta a wayata nayi Saved ina ta tunanin yadda zanyi sai aka dauke wayar tawa.

ina so zan koma wajansa yakara fadamin so Allah bai nufaba har ya kwanta rashin lapiya daga baya Allah ya dauki ransa is the last hope Wanda zan iya samun ‘yar uwata ZARA.

MATAN KA NAWA ?

Bani dasu Idan Kace mata ai da yawa gaskiya neh amma kasan Kana taka Allah yana tashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu