Kannywood

Bayani kan jaruman kannywood da suke yana kasar Cameroon  da yadda suka shigo kannywood.

Wasu na zaton cewa kusan dukkan jaruman kannywood yan kassr Nigeria amma ba haka abin yake ba, akwai wasu jaruman masu yawa da suke yana wasu kasar da yake ba Nigeria ba.

AMINA AMAL

jaruma amina amal an haifeta a kasar kamaru a garin bamenda inda tayi karatunta na firamare da kuma sakandirenta a kasarta kamaru, a yanzu kusan kowa yasanta a duniyar kannywood a sanadiyar wani rasin jituwa da suka taba samu sakaninta da jaruma hadiza gabon.

jaruma amal tasha matukar wahala kamin ta kasance jaruma a matsana’antar kannywood, inda a farko iyayenta suka ki amincewa da kudirinta na zamantowa jaruma, dan a lokacin ko yaren hausa ba ji take ba, daga karshe dai iyayenta suka amince, nan ta koyi yaren hausa sannan ta tsallake zuwa kasar nigeria ta fada hannun jarumi adam a zango,

Inda shi ya fara haskata a fim dinta na farko mai suna AMAL, a dalilin fitowarta a wanna fim ta amal yasa ake mata lakabi AMINA AMAL, ga masu bibiyanmu a wannan tashar tamu ta gaskiya24 zasu ga mun taba yin bidiyo akan jaruman kannywood da suke ba yan kasar nigeria ba, da irin wahalhalun da suka sha kamin su zama jarumai, a bidiyon munyi cikekken bayanin kan wahalhalun da ita jarumar amina amal tasha kamin ta zamo jarumma a kannywood.


 
RASHIDA LABBO


kusan duk mai bibiyan shirye shiryen tashar arewa24 masu dogon zango zai san RASHIDA LABBO domin ta fito a wani shirinsu mai dogon zango mai suna labarina, inda ta taka rawa matsayin kawar layla a cikin shirin, tayi suna sosai a kwananan ta hanyar wannan shirin ta arewa24 mai suna labarina.

Tsohuwar jarumar mai suna Rashida Lobbo ta zanta da fim magazine bayan da tayi shekara daya ba a ji duriyarta ba a masana’antar. Amma kuma bayan rashin ganinta, Rashida ta wallafa hotunanta a shafukanta na sada zumuntar zamani a kasar Thailand.

Kamar yadda tsohuwar jarumar ta bayyana, ita haifaffar kasar Kamaru ce kuma tayi karatu a Najeriya inda ta zauna da ‘yan uwanta a Abuja. Rashin cikar burinta na zama ma’aikaciyar gidan talabijin yasa ta fada harkar fim.

Tayi fina-finan Hausa da na turanci a masana’antar Nollywood. A zantawar da aka yi da Rashida, ta bayyana cewa tayi aurene kuma suna zama tare da mijinta mai suna Abubakar dan asalin kasar Mali, a birnin Bangkok dake Thailand.

Jarumar tace sana’ar mijinta siyar da gwal kuma yayi shekaru 26 a kasar Thailand. Kamar yadda Mujallar Fim ta ‘Fim Magazine’ ta bayyana, Rashida ta ce tana matukar kewar abokan aikinta na masana’antar fim kuma tana kewar mahaifiyarta don tun a 2018 da tayi aure bata sake zuwa Najeriya ba.

Da aka tambayeta dalilin da yasa ta bar masana’antar kuma tayi aure a sirrance, jarumar ta ce saboda lamarin rayuwarta ita kadai ya shafa. Tana jin harshen faransanci ne saboda mahaifiyarta na kasar Kamaru kuma tana zuwa hutu. Harshen turanci kuwa tana jinshi ne saboda karatun da tayi a Najeriya.


 
ANAN BAMENDA


yawancin jaruman kannywood HAUSA FULANI ne, sannan akwai da yawa daga cikin jaruman kannywood da suke ba yan kasar nigeria, daya daga cikin matasan jaruman kannywood da tauraruwarsu ke haskawa a wannan zamaninm mai sunan adnan bamenda, an haifeta a kasar kamaru sannan a can ta girma.

adnan tazo kasar nigeria domin cikar burinta na zamantowa jarumar finafinai, ta shiga masana’antar kannywood ta hanyar babban jarumin kannywood wato adam a. zango, inda ake hasashen ta fara fitowa ne a sabon shirinsa mai dogon zango, wanda aka sanyawa suna FARIN WATA SHA KALLO.

wannan jarumar kamar yadda muka fada haifaffiyar kasar kamaru ce kuma a can ta girma shi yasa ma ake mata lakabi da sunan garin da tafi a kamaru wato bamenda.


 

JAMILA GAMDARE


a sabon shirin gaskiya24 tv na kawo muku jaruman kannywood da suke ba yan kasar nigeria ba, a bidiyonmu na farko mun kawo muku jaruman kannywood da suke yan kasar nijer da kuma bayanai akansu, wannan shine bidiyo na biyu a cikinsa zamu kawo muku bayanai kan jaruman kannywood da suke yan kasar KAMARU.
Kalli a bidiyo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu