Kannywood

Tattaunawa Da Stephanie Daɗin Kowan Akan Rayuwar Ta Da Baku Sani Ba. Iya Niger Na Taɓa Zuwa

YA AKA YI KIKA SHIGA DADIN KOWA ?

Kawaii ina cikin zaman zama na sai naga postin na arewa24 Lokacin ma ina karatu Suna neman sabbin Jarumai don a fara wannan sabon salo Wanda ya shige saina zo nayi

audition sai Allah yasa aka dace an aka fara a sabon salo kashi muna yi har a ka zo WASA FARIN GIRKI gashi muna kanyi har yanzu.

WADANNA TAMBAYOYI A KAFI YI MIKI ?

Idan aka ganni sai a ce ga stephanie sai suce ina nasir Ina madam gloria Kani suke mu kwana muke gida daya duk yan dadin kowa a ce min Ina I b ina nasir dama nasir a

kafi tambayana wai bada Gaske kuke soyayya bah kuma ba sanshi kike bah abun da a kafi tambaya ta kenan.

TSAWON WANNA LOKACI KIKE DAUKA A WANKA DA KWALLIYA ?

Tohh, ni problems Dina kenan idan nashiga wanka kabani minti biyu na gama kuma idan na fito bana kwalliya ma abun yana Bani wuta nadau kayan make-up na zazzana saboda beauty dinnan kyan mace yana jikinta nayi

shekara daya 1 bana saka jambaki so inajin hakan nafi kyau nafi kowa kyau gaskiya to yanzu ya na karata idan na shafa dukkanin Abu-buwan a she traffic zanja kenan haka nake ji haka nafi kyau gaskiya.

WANE IRIN KAYA KI KA FI SO ?

Doguwar Riga amma ina saka riga da sketch ma da gaskiya nafison kananan kaya bamani da atamfa da saidai a dauki kayan a kaiwa tailor a dinka sannan a kawo min to amma yanzu girma yazo.

BERA KO MAGE KO KYANKYASO KO KADANGARE ?

Gaskiya ina tsoro dukka amma kyankyaso da sauki idan na gani bana gudu idan na gani bana firgita sosai amma na tsani mage saboda gani nake idan naga mage zanyi mafarki anjima.

KASASHE NAWA KI KA TABA ZUWA ?

Amma kar kace min ‘yar kauye ni iya Niger na taba zuwa.

WADANNE BURIKA KIKE DASU ?

Burina da yawa gaskiya amma tinda ni Business woman ce ina so na shahara da kudin halak sannan matakina na acting shima ina so inci gaba sannan ina son luxury life yanzu ana nema dai amma gobe ina so naji ance antara kudi sosai muna hawan G-Wagon.

Kasance da *Manuniya.com domin samun sabbin labaran kannywood dan samun nishadin Ku . Saboda jin dadinku shine namu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu