Labarai

Za a fara biyan kudi a shafukan Facebook da Instagram.

Za a fara biyan kudi a shafukan Facebook da Instagram.

Kamfanin Meta da ke da kafofin sada zumunta na zamani na Facebook da Instagram ya sanar a wannan Lahadin cewar zai kaddamar da wani tsari ga mai bukatar tantance shafinsa ko dai na Facebook ko kuma na Instargram. Sai dai tsarin zai bukaci biyan wasu ‘yan kudade.

Shugaban Kamfanin Mark Zuckerberg ya ce sun fito da wannan tsarin ne domin kaucewa masu amfani da hotunan ko sunayen wasu mutanen na daban suna cewa su ne, wanda a lokuta da dama har ta kan kai ga an yi damfara da sunan wani da bai ji ba bai gani ba.

A ko wane wata alamar ta tantancewar ta Meta za ta kai dalar Amirka 12 ko kuma 15 kwatankwacin naira dubu 5 ko kusan dubu 7 ga kowane shafi.


Mark Zuckerberg ya ce wannan sabon shirin zai fara aiki ne a wannan makon da muke shiga a kasashen Australiya da NewZealand kafin daga baya su isa wasu kasashen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button