Labarai

Buhari ya saka hannu kan dokar kafa majalisar mika mulki ga shugaban kasa.

Buhari ya saka hannu kan dokar kafa majalisar mika mulki ga shugaban kasa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan wata doka ta zartarwa kan sauwaka da gudanar da sauye sauyen shugaban kasa. Buhari ya ce hakan zai kara inganta mika mulki daga gwamnatin shugaban kasa zuwa wancan.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka tabbatar ta shafinsa na Twitter ranar Alhamis.

Shugaban ya kuma bayyana cewa ya amince da kafa kwamitin mika mulki na shugaban kasa, wanda sakataren gwamnatin tarayya, SGF zai jagoranta.

Buhari ya rubuta: “Na rattaba hannu kan dokar zartarwa mai lamba 14 na shekarar 2023 kan Saukakewa da Gudanar da Canjin Shugaban Kasa.

Sabuwar Dokar Zartarwa ta kafa tsarin doka don mika mulki gadan-gadan daga wannan Gwamnatin Shugaban kasa zuwa waccan.

“Na kuma amince da kafa kwamitin mika mulki na shugaban kasa, wanda sakataren gwamnatin tarayya (SGF) zai jagoranta, don saukakawa da kuma gudanar da shirin mika mulki ga shugaban kasa a 2023.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button