Labarai

Kamfanin BUA Ya kashe N116bn Titin Kano Daga Kazaure Zuwa Kongolam

Kamfanin BUA Ya kashe N116bn Titin Kano Daga Kazaure Zuwa Kongolam.

Kamfanin BUA ya kaddamar da aikin fadada hanyar Kano zuwa Kazaure-Kongolam mai tsawon kilomita 132 tare da hadin gwiwar ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya.

Wannan matakin ya yi daidai da umarnin shugaban kasa mai lamba 007 kan bunkasa ababen more rayuwa da tsarin bada harajin zuba jari na gyaran hanya, wanda ya ba da hakin haraji ga wasu ’yan asalin kasar don gudanar da gyare-gyaren manyan titunan gwamnatin tarayya.

Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola ne ya kaddamar da aikin na Naira biliyan 116 a wani biki a Kazaure na jihar Jigawa.

Sanarwar da BUA ta fitar ta ce, aikin zai ratsa jihohin Kano, Jigawa, da Katsina daga titin Dawanau a jihar Kano zuwa Kongolam a jihar Katsina.

Ministan, a cewar sanarwar, ya bayyana cewa, kamfanin BUA Group ne zai kasance mai kudin aikin gina hanyar mai tsawon kilomita 132 a wani bangare na ci gaba da ayyukan raya ababen more rayuwa.

Da yake jawabi a wajen bikin, Babban Daraktan Rukunin na BUA, Kabiru Rabiu, ya ce BUA ta ci gaba da jajircewa wajen hada kai da gwamnati kan muhimman ayyuka da tsare-tsare da za su hanzarta samar da ci gaban bil’adama, zamantakewa, da samar da ababen more rayuwa a fadin kasar nan.

Rabiu ya ce kungiyar BUA wadda ita ce ke ba da kudin aikin, tuni ta hada kayan aiki zuwa wurin kuma tana da iya aiki da kwarewa da kuma kayan aikin da za ta iya kammala hanyar a kan tsari.

Ya kuma mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministan ayyuka da gidaje bisa amincewa da aikin tare da jaddada kudirin kungiyar na samar da hanyar mota guda biyu wadda za ta kasance cikin mafi inganci a nahiyar Afirka.

Fashola ya ce babban titin da kamfanin BUA Group ke ginawa tare da samar da ababen more rayuwa, zai karawa ayyukan gina layin dogo da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a shiyyar Arewa maso Yamma a Najeriya tare da kara bude kofa ga Najeriya da ma babban yankin yammacin Afirka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu