Kannywood
Albashin Jami’an yan sandan Nijeriya daga matakin farko har zuwa karshe.
Duk wani Jami’in dan sanda yana aiki ne don tabbatar da doka da oda a yankunan karkara ta hanyar kare jama’a da dukiyoyinsu, hana aikata laifuka, rage tsoron aikata laifuka da inganta rayuwa ga dukan ‘yan ƙasa.
Wata ₦50,702.
Shekara ₦608,429
Sun kasance matakin farkon a aikin police Su ne yawanci ake turowa, zu kamo kananun masu laifi da bincikan ababen hawa akan titin da da dai sauran.
- Police corporal.
Wata ₦70,188
Shekara ₦842,256
Yana daya daga aikin corporal shine ayyukan sintiri, sa ido da gudanar da aikin bincike da kuma tabbatar da an bi umarnin da manyan su suka ba su.
- Police sergeant
Wata ₦98,596
Shekara ₦1,183,147
Sergeant shine babban mai sanya idanu akan ayyukan abokan aikinsa shin suna aikinsu da kyau, da kuma tabbatar da kowa yana kan aikinsa.
- Police sergeant major.
Wata ₦149,378
Shekara ₦1,796,861
Kusan aikin su guda da sergeant amma shi yana turo da rahotanni masu mahimmanci ga manyan su.
- Police inspector
Wata ₦160,294.
Shekara ₦1,923.523
Ya kasance mai gudanar da kula da tawagar jami’an ‘yan sanda kan kiyaye doka da oda da bincikar laifuka, da kuma amsa tambayoyi daga jama’a.
- Assistant superintendent ASP
Wata ₦174,499
Shekara ₦2,091,990
Ya kasance mai kula da reshen yanki ne, shi yake dauke da nauyin kula duk wani aiki da ya danganci manyan ta’addanci, a duk inda aka aikata wani babban laifi dole ya kasance a wajen
- Deputy superitendent DSP
Wata ₦189,451
Shekara ₦2,273,414
yana aiki a karkashin S.P kuma yana kula da duk wasu ayyuka na hukumar ‘yan sanda kamar hana aikata laifuka, gudanarwa da kula da ofisoshin ‘yan sanda, kula da bincike da sauransu. - Superitendent of police sp.
Wata ₦223,490
Shekara ₦2,681,885
Yana taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da aikin ƴan sanda a bangaren manyan al’amura ko abubuwan da suka faru; tsarawa da jagorantar ayyukan cikin layi tare da tsarin doka, da cimma manufofin ‘yan sanda don tabbatar da doka da amincewar jama’a
- Chief superitendent
Wata ₦247,833
Shekara ₦2,963,955
Ya kasance mai gudanar da bangarori daban-daban masu fadi, yana da nauyin duk wani aiki babba da za’a gudanar a yankin da yake da kuma kewayen wajen.
- Assistant commissioner
Wata ₦279, 289
Shekara ₦3,351,470
Mataimakin Kwamishinan yana da Alhakin yin ko wanne irin aiki a yankinsu, sannan yana aiki tare da sauran mataimakan kwamishinoni don tabbatar aikin su yayi kyau da kuma sun tabbatar da ko wanne umarni a daidai yake tafiya, sun maida hankali akan manyan abubuwa.
- Deputy commissioner
Wata ₦306,946
Shekara ₦3,683,347
yana da alhakin kiyaye doka da oda. Shi ne shugaban hukumar aikata laifuka kuma yana kula da duk Majistare na zartarwa. Sannan sarrafawa da jagorantar ayyukan ‘yan sanda.
- Commissioner of police.
Wata ₦620,044
Shekara ₦7,440,523
Shine yake da Alhakin lura da jihar da yake, da kuma ganin an tabbatar da zaman lafiya da kuma bi doka a jihar
- Inspector general
Wata ₦1,126,294
Shekara ₦13,515,523
Shine mukami na kololuwa a aikin dan sanda a Nigeria, shine shugaban yan sanda na kasa.