Siyasa

Tofah! Hukuncin Da Kotu Zata Yanke Akan Zaɓen Kano Ba Lallai Ya Yiwa Yan Kwankwasiyya Dadiba Inji…

Tofah! Hukuncin Da Kotu Zata Yanke Akan Zaben Kano Ba Lallai Ya Yiwa Yan Kwankwasiyya Dadiba.

GA CIKAKKEN BIDIYON A NAN ƘASA 👇

Matashin Kano Daya Yi Wuf da Ba’amurkiya Ya Shiga Rundunar Sojin Amurka

Wani dan jihar Kano mai suna Suleiman Isah da ya auri wata Ba’amurkiya mai shekaru 46, Janine Sanchez, ya shiga cikin rundunar sojan kasa ta California, da ke Amurka,kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Dangane da bayanan, Rundunar Sojan Kasa ta California ta ƙunshi sojoji 18,450

MANUNIYA

ta rawaito cewa masoyan biyu, wadanda suka hadu a shafukan sada zumunta, sun yi aure ne a ranar 13 ga watan Disambar shekarar 2020.

Misis Janine, wata mai dafa abinci ce da ke birnin Lindon na jihar California, ta je Najeriya domin bikin auren su.

Daurin auren wanda ya gudana a Masallacin Juma’a na barikin MOPOL na 52 da ke Panshekara a karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano, ya samu halartar dubban jama’a daga ciki da wajen Jihar Kano.

Wani tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, wanda kuma dan uwa ne ga mahaifin angon, ya tsaya a matsayin wakilin Janine wato (waliyi).

Da yake tsokaci kan wannan sabon lamari a shafinsa na Facebook, Sani ya taya jami’in murna, wadanda suka caccake shi a lokacin da yake goyon bayan kungiyar.

“Sun soke ni kan wannan auren kuma yanzu Suleiman Isah ya yi aure cikin farin ciki kuma ya shiga cikin rundunar sojan California ta kasa. Ina taya murna,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu