Siyasa

DA DUMI – DUMI: Dalilin Da Ya Sa Na Nuna Katin Zabe Na, na zabi Tinubu Cewar – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya fito fili ya nuna katin zabe bayan ya kada kuri’a a garin Daura na jihar Katsina.

Buhari ya ce ya fito fili ya fito da katin zabensa domin ya nuna cewa ya zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu.

Ya ce baje kolin katin zaben shi ne domin nuna goyon bayan sa ga jam’iyyar.

Buhari ya bayyana farin cikin sa kan yadda jama’a suka fito a lokacin zaben.

A cewar Buhari: “A ko’ina na ambaci dan takarar da na fi so, Asiwaju Tinubu, kuma na yi imanin mazabana za su zabe shi dari bisa dari.

’Yan Najeriya su tabbatar an mutunta su; hakan na nufin dan takarar da suke so su zabe shi ya halatta su zabe shi.”

Kafin zaben na ranar Asabar, an yi ta rade-radin rashin jituwa tsakanin Buhari da Tinubu.

Tinubu ya zargi gwamnatin Buhari da yin amfani da sabon tsarin Naira da kuma karancin man fetur wajen kawo cikas ga burinsa na shugaban kasa.

Sai dai Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su zabi Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu