Siyasa

Gwamnan Kwara Ya Dauke Wa Dalibai Da Talakawa kudin Mota Tare Da Ba Su Tallafin kudade

Gwamnan Kwara Ya Dauke Wa Dalibai Da Talakawa kudin Mota Tare Da Ba Su Tallafin kudade.

Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince a rika daukan dalibai da ‘yan fansho da sauran jama’a talakawa masu rauni kyauta a motocin haya na bas domin rage musu radadin wahalan karancin mai da na naira.

Haka kuma gwamnan ya amince a rika bai wa matan da mazajensu suka rasu da ‘yan fansho da masu motocin sufuri da ‘yan kasuwa da kananan manoma da sauran talakawa a jihar taimakon kudi, inda za a rika tura musu kudin.

Ya ce hukumar shirin bunkasa rayuwar jama’a ta jihar ce (Kwara State Social Investment Programme wato KWASSIP ), za ta aiwatar da shirin tainmakon.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Rafiu Ajakaye, ya fitar a jiya Alhamis, ya ce gwamnan ya umarci KWASSIP ta gaggauta tsara yadda za a gudanar da shirin domin saulkaka wa jama’a halin da suke ciki.

A sanarwar, ya ce, gwamnan ya kuma bayar da umarnin sanya motocin bas-bas na kyauta a wasu hanyoyi da dalibai da malaman manyan makarantu suka fi bi a babban birnin jihar, inda aka fi shan wuyar rashin man.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu