Siyasa

Labari Da Dumi Dumi Mataimakin Gwamnan Sokoto ya fice daga PDP

Mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Manir Muhammad Dan Iya ya mika takardar murabus dinsa daga shugabancin jam’iyyar PDP.

Walin Sokoto, a wata takarda mai dauke da kwanan wata 8 ga Fabrairu 2023 kuma ya aika wa Shugaban gundumarsa ta Kware, karamar hukumar Kware, ya ce yana sanar da shugabannin Jam’iyyar murabus dinsa.

Wasikar da Manuniya, ta gani mai suna “Wasikar ficewa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party.

Wasikar da DAILY POST ta gani mai suna “Wasikar ficewa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party.

An rubuta cewa, “Na rubuta ne domin sanar da ku ficewar daga jam’iyyar Peoples Democratic P’arty (PDP) daga ranar 8 ga Fabrairu 2023.

“Na yaba da damar da aka bani, wanda ya sanya na yi aiki a mukamai daban-daban a karkashin jam’iyyar PDP.

“karba gaisuwata.”

Wannan na zuwa ne cikin ‘yan sa’o’i kadan a taron jam’iyyar All Progressives Congress, APC a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu