Siyasa

Na Daina Damuwa Da Rikicin PDP – Atiku Abubakar

Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce ba shi da wata damuwa dangane da rikicin cikin gida da ya addabi jam’iyyarsu ta PDP.

Ya kara da cewa a halin da ake ciki, mawuyacin al’amari ne iya canza shugabancin jam’iyyar.

Atiku ya yi wadannan kalaman ne yayin tattaunawar da VOA Hausa kwanan nan a Amurka.

A cewar Atiku, “Har yanzu ba mu cimma masalaha ba amma mun ci gaba da harkokinmu, ba ni da wata damuwa dangane da haka.”

Ya kara da cewa, “A kan wannan gaba, ba daidai ne ba a dauko batun canjin shugabancin jam’iyyar alhali zabe na karatowa.”

Idan dai ba a manta ba, wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka hada da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas da takwarorinsa na Binuwai da Oyo da Inugu da Abia da sauransu, sun shiga takun saka da Atiku kan bukatar canja Shugaban PDP na Kasa, Iyorchia Ayu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu