Siyasa

Ƙarancin kuɗi Buhari Ya Gana Da Emefiele Da Tambuwal Da Bagudu

Ƙarancin kuɗi Buhari Ya Gana Da Emefiele Da Tambuwal Da Bagudu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da shugaban ƙungiyar gwamnoni ta Najeriya Aminu Waziri Tambuwal, da shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC Atiku Bagudu kan matsalar ƙarancin sabbin takardun kuɗi da ƙasar ke fuskanta.

Daga cikin waɗanda suka halarci zaman har da gwamnan Babban Bankin ƙasar Godwin Emefiele da shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar Abdulrasheed Bawa da kuma babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasar Janar Lucky Irabor.

An yi ganawar ne a fadar shugaban ƙasar da ke Abuja.

Da farko an tsara zaman da ƙungiyar gwamnonin ƙasar, to sai dai daga baya an soke zama da duka gwamnonin sakamakon wasu dalilai da ba a bayyana ba.

Bayyanar gwamnan Babban Bankin a ganawar alama ce da ke nuna cewa an tsara zaman ne domin tattauna batun matsalar ƙarancin kuɗi, da ke fuskantar suka daga ‘yan ƙasar, ciki har da gwamnonin ƙasar.

A makon da ya gabata ne dai shugaban ƙasar ya gana da ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, inda wasu daga cikin gwamnonin suka yi kira ga shugaban ƙasar da ya shiga tsakani domin bayar da dama a ci gaba da amfani da tsoffi da abbin takardun kuɗin a faɗin kasar.

To sai dai rahotonni sun ce shugaban ƙasar ya yi watsi da buƙatar kasancewar kotu ta haramta wa gamnati sake ƙara wa’adin daga ranar 10 ga watan Fabrairu.

Wasu majiyoyin a fadar shugaban ƙasar sun tabbatar da cewa shugaban ƙasar na kaffa-kaffa, kada ayi masa kallon mai watsi da dokoki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu