Siyasa

2023: Ta Faru Takare – Wike ya sakecewa Gwamnonin G-5 ba za su taba zama da Atiku ba.

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce babu wata dama da shi da abokan siyasar sa za su iya tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, kafin babban zabe.

Wike ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da manema labarai a Fatakwal ranar Alhamis.

Kungiyar gwamnoni biyar da aka fi sani da G5, karkashin jagorancin Wike na adawa da takarar Atiku.

Abokan sa sun hada da Seyi Makinde na Oyo, Samuel Ortom na Benue, Okezie Ikpeazu na Abia, da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

Wike ya yi iƙirarin cewa lokacin warware korafe-korafen G5 ya ƙare “kuma bai shirya sake zama da kowa ba”.

“A’a, ba za mu iya yin haka ba; an kare! Mun fadi hakan kuma babu wani abu da kowa zai iya yi a kai yanzu,” inji shi.

“Sun yi imanin za su iya lashe zaben. Ban shirya sake zama da kowa ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button