Siyasa

Hotunan ganawar Buhari da Tinubu, Shettima, Gwamnonin APC

Hotunan ziyarar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima suka kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, a garin Daura na jihar Katsina.


Tinubu da Shettima sun taso ne daga Abuja ranar Laraba ‘yan sa’o’i kadan bayan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ba su takardar shaidar cin zabe.

Naija News Hausa ta samu cewa shugabannin biyu da wasu gwamnonin da aka zaba a jam’iyyar APC sun abkawa garin Daura ne domin nuna godiya da kuma jinjinawa shugaban kasar kan goyon bayan da ya bayar a lokacin yakin neman zabe.

Tinubu ya samu rakiyar Shugaban Gwamnonin APC kuma Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu a ziyarar godiya ta musamman; Gwamna Dapo Abiodun na Ogun; Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna da Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila.

Sauran sun hada da Gwamna Dave Umahi na Ebonyi; Gwamna Bello Matawelle na Zamfara; Gwamna Abubakar Badaru na Jigawa; Gwamna Aminu Masari na Katsina; Gwamna Sani Bello na Nijar; da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu