Siyasa

Gwamnonin APC Kudu Maso Yamma Zasu Gana Da Bola Tinubu A Oyo

A yau Alhamis ne gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC za su gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a birnin Ibadan na jihar Oyo.


Manuniya ta rahoto cewa hakan ya fito ne a wata sanarwa a ranar Laraba ta hannun Kehinde Olaosebikan, kakakin majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a Oyo.

Idan dai za a iya tunawa jam’iyyar APC ta tsayar da ranar 7 ga watan Fabarairu ne za a gudanar da babban taronta na shugaban kasa amma sai da ta sake shirya shi saboda rikicin da ya biyo bayan matsalar Naira da kuma karancin man fetur.

Olaosebikan ya ce kwamitin shirya gangamin na karamar hukumar da aka shirya a dakin taro na Mapo mai dimbin tarihi a ranar Alhamis ya kammala dukkan shirye-shiryen taron.

Yayin da yake bayyana cewa Tinubu zai kaddamar da shirye-shiryensa na jihar da Najeriya, Olaosebikan ya kara da cewa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, zai jagoranci mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar a fadin Najeriya.

Ya ce an samar da isassun matakan tsaro a ciki da wajen taron, yana mai jaddada cewa shirin zai tabbatar da tsaron lafiyar mutane da dukiyoyinsu.

A cewar Olaosebikan, zirga-zirgar mutane da ababen hawa za su kasance cikin sauki kamar yadda ya kamata a duk titunan da jirgin yakin neman zabe ya ziyarta.

Ya ce gwamnoni da ministoci da sauran jiga-jigai da Teslim Folarin, dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar za su tarbe Tinubu da Shettima a filin jirgin saman Alakia.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button