Siyasa

Da Dumi Dumin Sa El Rufai Yace Baiyi Imani Da Shugaban Kasa Buhari Ba Ya Kamata Kusan Wannan

Gwamna El-Rufai ya caccaki fadar shugaban kasa a wata hira da jaridar Premium Times ta fitar ranar Lahadi.

Yayin da yake bayyana cewa bai yarda da “ingantattun shawarwari” da wadanda ke kusa da Shugaban kasar suka dauka ba, gwamnan, ya ce har yanzu ya yi imani da Buhari.

El-Rufai ya ce: “Na yi imani da Buhari. Har yanzu ina yi kuma ba zan daina gaskata shi ba. Amma na daina yarda da da’irar da ke kewaye da shi da ingancin yanke shawara da ayyukan da ke fitowa daga wannan shugabancin. “

Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya ne gwamnan Kaduna ya caccaki na kusa da shugaban kasar sakamakon cece-kucen da ya kunno kai dangane da batun sauya fasalin Naira.

El-Rufa’i, wanda ya yi ta tofa albarkacin bakinsa kan rikicin musayar kudi, ya yi ikirarin cewa akwai masu zagon kasa a gwamnatin Buhari da ke kokarin ganin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta gaza a zaben shugaban kasa.

Ya ce: “Yawancin mutanen da ke cikin villa ba ’yan jam’iyyarmu ba ne. Na yi imanin akwai wasu abubuwa a cikin Villa da ke son mu fadi zabe saboda ba su da hanyar da za su bi,” in ji El-Rufai.

Suna da ‘yan takararsu, kuma ’yan takararsu ba su ci zaben fidda gwani ba kuma ina ganin har yanzu suna kokarin ganin mun fadi zabe kuma suna fakewa da burin shugaban kasa na yin abin da yake ganin ya dace.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu