KannywoodLabarai

Nayi Dana Sanin Ɗaukar shirin Yan Tiktok zango na farko – Mujahid M Soja

Mamallakin shirin film din YAN TIKTOK kuma Daraktan shirin wato (MUJAHID M. SOJA) ya bayyana takaicin daukar zango na farko a lokacin da yake daukar zango na biyu na shirin, inda ya bayyana dalilansa kamar haka

“Daraktan yace tun daga yadda ya samar da labarin zango na biyu ya fara danasanin daukar zangon farko na shirin, domin kuwa matsalar labarin zango na biyu sunyi tunani sosai wajan kawo Abubuwa naban mamaki domin kuwa a zango na biyu ne aka fitar da labari na gaske wanda ya tsaru.

” Sannan a zango na biyu din ne aka fitar da ma’anar TIKTOK da matsalar sa da kuma alfaninsa ga Al’umma, kuma duk a cikin zango na biyun ya samar da 6angarori daban daban a cikin labarin, cikin 6angarorin da matsara labarin suka ta6a daga ciki Akwai fadakarwa, nishadantarwa, da zaman takewar aure da kuma uwa uba sun kalli zahiran na yadda ake ma’amalantar manhajar Tiktok din a wannan zamani

“Abu na biyu yace duba da yadda ya samar da kayan aikin daukar wannan shiri na YAN TIKTOK zango na biyu hakan ya sake jin dama tun farko ya samu damar da ya samu yanzu domin kuwa ya tabbar da na’urorin da yake aiki dasu a wannan karan na zamani ne kuma manya irin wadan da masana’antun shirya fina finai na duniya suke amfani dasu, ya chanzawa shirin kamanni ta kowanne 6angare a cewar sa, ta yadda dan kallo ma bazai yadda cewar zango na farko yanada Alaqa da zango na biyu ba saboda tsabar samun banbanci

A karshe yayi Godiya ga Allah da ya bashi ikwan yin zango na farko domin sai da ya yishi ne ya sake samun gogewar tunanin zamanantar dana biyun @real_mujahid_m.soja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!