Labarai

‘Yan Bindiga Sun Shiga Gidan Shugaban Kamfanin Three Brothers Sun Kasheshi Da Matarsa

‘Yan Bindiga Sun Shiga Gidan Shugaban Kamfanin Three Brothers Sun Kasheshi Da Matarsa.

A Yanzu Mun Samu Wani Rohoto Daga Shafin Hausa Legit Sun Rawaito Cewar Yan Bindiga Sun Shiga Gidan Shugaban Kamfanin Three Brothers Na Jigawa Sun Harbeshi Shi Da Matarsa.

ASP Lawan Shiisu, mai magana da yawun yan sandan jihar Jigawa, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai NAN hakan a ranar Litinin a Dutse.

Jaridai Guardian ta rahoto Shiisu ya ce lamarin yafaru ne a ranar 13 ga watan Nuwamba misalin karfe 2:30 na dare inda wasu da ake zargin bata gari ne suka kutsa gidan mamamcin a kauyen Kebberi suka bindige su.

Daya Ke Bayyana Lamarin Ya bayyana cewa wadanda ake zargin kwararrun
masu kisa ne sun bindige marigayin, mai suna Alhaji Musa da matarsa Hajiya Adama nan take.

Kakakin yan sandan ya ce wadanda ake zargin basu sata komai ba daga gidan wadanda abin Yafaru da su, wanda shine shugaban kamfaninThree Brothers Mill da ke Malammadori.

Ya ce:”A ranar 13 ga watan Nuwamba misalin karfe 2:30pm, wasu bata gari da ba a san ko suwanene ba sun kutsa gidan wani Alhaji Musa,Manajan kamfanin Three Brothers Rice Mill, suka bindige shi da matarsa Hajiya Adama, dukkansu yan kauyen Kebberi a karamar hukumar Malammmadori.”

A cewarsa an gano kwalin wayoyin salula biyu daga wurin da abin ya faru, ya kara da cewa an kama mutane biyar da ake zargi da hannu kumaana musu tambayoyi, The Nation ta ruwaito.

Shiisu ya kara da cewa ana cigaba da
kokari domin kamo wadanda ake zargi domin su girbi abinda suka shuka.

Zamu So Ku Watsa Labarin Nan Domin Yaje Kunnen Mutane Dayawa Da Basu San Halin Da Ake Ciki Ba, Sannan Kada Ku Manta Ku Ajiye Mana Ra’ayoyinku Akan Wannan Rohoto, Idan Wannan Shine Farkon Shigowarka Wannan Shafi Munaso Ka Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu