Labarai

Muna Goyon Bayan Takarar Tinubu —Shugabannin Fulani

Shugabannin Fulani daga sassa daban-daban na Najeriya sun jaddada goyon bayansu ga dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Tinubu a kafafen sadarwa na zamani, Abdulaziz Abdulaziz ya fitar.

Sanarwar ta ce shugabannin Fulani da ake kira da Ardo, sun bayyana goyon bayan ne a wani taro da suka gudanar a Abuja a ranar Lahadi.

A taron da suka yi tare da hadin kan kungiyar sabuwar Arewa wato “Arewa New Agenda” shugabannin sun yi alkawalin yin amfani da ’ya’yan kungiyar 33,661 wajen janyo kan sauran ’yan uwansu Fulani domin su zabi Tinubu a zaben da ke tafe.

A jawabinsa bayan an kammala al’adar Fulani ta rabon goro ga mahalarta taron, shugaban kungiyar, Aliyu Liman Bobboi, ya ce raba goron da aka yi yana nufin shugabannin za su koma gida su isar da sakon shawarar da aka yanke a wajen taron ga mabiyansu.

Ya kara da cewa, an gudanar da taron ne domin nuna wa duniya goyon bayansu ga Tinubu saboda sun yarda kuma sun yi amanna da cancantarsa, dalilin da suke masa addu’ar samun nasara a zabe mai zuwa.

Ya bayyana cewa a matsayinsu na shugabanni, suna da ta cewa sosai a kan wanda mutanensu za su zaba, kuma suna da yakinin cewa magoya bayan nasu za suyi masu biyayya.

Liman ya ce makusanta shakikai da ke tare da Tinubu kamar Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, Gwamna Abubakar Badaru na Jigawa, tsohon shugaban EFCC Malam Nuhu Ribadu, da sauran manyan Fulani, wata manuniya ce ta yadda Tinubu ya dauki kabilar Fulani da muhimmanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu