Labarai

Gwamna Masari Ya kafa kwamitin Binciken kisan Yan Sa kai Sama da 100 a Katsina

Gwamna Masari Ya kafa kwamitin Binciken kisan Yan Sa kai Sama da 100 a Katsina.

Gwamnan jihar Katsina da ke arewa maso yamacin Najeriya Aminu Bello Masari ya kafa kwamiti mai mambobi 13 da zai gudanar da bincike kan kisan ‘yan sa kai sama da 100 da aka yi a wasu garuruwan ƙananan hukumomin Kankara da Bakori a jihar.

A wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwamnan Al-amin Isa, ya aike wa manema labarai, ya ce ana sa ran kwamitin ƙarkashin jagorancin Hon. Justice A.B. Abdullahi, zai gudanar da bincike domin gano abun da ya haddasa kashe-kashen a waɗannan garuruwa.

Sauran ayyukan da ake sa ran kamitin zai gudanar sun haɗa da yin bincike domin gano adadin rayuka da dukiyoyin da ka rasa a lokacin kashe-kashen.

Tare da gano yawan mutanen da harin ya shafa sannan da gano ƙungiyoyi ko mutanen da ke da suka aikata ko suke da hannu wajen wannan aika-aika.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnati na duba yiyuwar tallafa wa waɗanda lamarin ya rusta da su tare da iyalan mamatan, da bayar da shawarar ɗaukar matakan kare kai da bai saɓa wa doka ba, tare da ɗaukar matakai domin kare aukuwar makamancin wannan hari a nan gaba a jihar.

A makon da ya gabata ne dai rahotonni suka ce ‘yan bindiga sun yi wa wasu ‘yan sakai waɗanda ke ƙoƙarin ƙwato wasu shanun sata, kwanton ɓauna tare da kashe sama da 100 a wasu garuruwa a ƙananan hukumomin Kankara da Bakori a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu