Kannywood

Tattaunawa da Diamond Zahra akan rayuwar ta da kalubalen da ta fuskanta da zai baku matukar mamaki

Meye sunanki ?

Sunana Zahra Mohamed, wacce aka fi sani da Diamond Zahra.

Me ya sa ake ce miki Diamond Zahra ?

Lakani ne kawai.

Yaushe kika shigo kannywood ?

Nashigo masana’antar Kannywood tun 2018,

kuma na fara da fim din farko da ake ce masa Zuma da Madaci.

Yaya akayi kika shiga ?

Da yake ina son fim tun ina yarinya, ni nakawo kaina ba wani ba.

Kin fuskanci wani kalubale kafin a karbe ki ?

Ai fim sana’a ce , kuma kowacce sana’a tana bukatar raino,

kuma ko wacce sana’a tana da na ta matsalolin.

Wa ya raine ki ?

Auwal D. Yakasai

Kin yi fim sun kai nawa ?

Zuma da Madaci, Wakili, Laifin Wani, Mardiyya, Barista Kabir, Gargada, Sirrin So… Kusan dai takwas haka.

Wanne Kika fi so a cikinsu ?

Zuma da Madaci. Sabo da shi na fa ra yi kuma ni ce naja wannan fim din.

Da ma ce aka ba ni a matsayina na sabuwar actress (jaruma) sannan aka hada ni da manyan jarumai. Sabo dahaka , har gobe shine fim din da nafi so.

Wanne ya fi ba ki wahala ?

Gargada, shi ba fim bane, series ne amma na sha wahala saboda yawancin sena senan (scenes) a kan hanya ne ba agida ba ne. Kuma series ne mai dauke da guje guje, makirci, kuka da dai sauransu. Sabo da haka, shi yafi bani wahala.

Kwadayi ko rowa ko munafunci, wanne ne halin ki a cikinsu ?

Ni dai gaskiya ba’ataba zuwa ance min ga wanda nake da shi ba. Amma dai ka san dan Adam ba’a iya masa.

Kyauta ko hakuri ko yafiya ?

Ina da kyauta, ina yafiya, sai dai hakurina kalilan ne.

Wane abu ne ya ke burge ki ?

Abin da nake so shi ne mutum ya so ka da mugun halin ka da kuma kyakkyawan halin ka. Idan hakan ta kasan ce, nomal zan iya zama da kai

Kasashe nawa kika taba zuwa ?

Nii kasashen da nataba zuwa sune: Nigeria, Niger da Faransa.

An taba galla miki mari ?

Hmm! A fim aka taba galla min mari. Lokacin ina son hawaye ya fitomin , sai na ce a galla mini mari. Amma naji haushi sossai daga baya.

Wanne irin abinci kika fi so ?

Abincin da na fi so shine tuwo da miyar kubewa. Sabo da ance kowa yabar gida, gida ya barshi. Tuwo shine abincin da za ka ci kaji ka koshi.

Me ye matakin karatun ki ?

Na gama secondry school amma a iya nan na tsaya. Na yi karatu ne a Nijar.

Ke ‘yar wace kasa ce?

Ni ‘yar Nijar ce, jahar Tawa.

Wace ce kika fi so a hada ku fim da ita ?

Wacce nake so a hada mu fim da ita, itace Zainab Indomi.

Tana burge ki Kenan ?

Sosai ma kuwa, har gobe, har ji bi, har abada.

Abdul M Sheriff, Gazzali Miko, Shamsu Dan Iya, wa kika fi so a hada ku fim ta re ?

Wanda nafi so a hada mu shine wanda sa’a ta hau kansa.

To cikin Zango ko Ali Nuhu ko Sadiq Sani Sadiq fa ?

To me ye zai hana a rubata labari a hada su su duka ukun.

An taba gulmarki maganar ta dawo kunnenki ?

Korai an taba yi. Amma ai ance kare baya haushi shi kadai, sai an tanka Mishi za asan yana yi. Sabo dahaka, duk wanda yayi gulmana a gaba na sai na ba shi am’sa

Za ki iya daina yin fim?

A farko dai lokacin ina yarinya, nasan ina sha’awar fim. Amma da na shigo harkar fim, sai na samu abu daya wanda shi ne rike da ni,

wato na dau fim a matsayin sana’a. Amma ko yau ko gobe nasamu abin da zai ri ke ne, abun da zai rufa min asiri, to zan iya barin fim.

Yi mana magana da harshen Faransanci mu ji ?

Mesdames et messieurs, je vous prie de regarder BBC Hausa sur Instagram, sur Twitter et sur tous les réseaux sociaux. Merci !!!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu