Magunguna

Yadda Zaku Magance Dattin Hunhu Ta Hanyar Amfani Da Karas

ZAKU MAGANCE KO WANKE DATTIN HUNHU.

Hunhu Abu ne dakan dau datti kasancewar iskar da muke shaka cikinsa take zuwa, musanman masu shan Tabar Sigari, Tabar Wiwi kokuma masu cin Goro dai dai nau’ikan abun da ka iya sawa Hunhu datti.

Hakan ne yasa muka binciko muku maganin da dakanku zaku hada don ku magance wannan datti da hunhu kan dauka ta ko wacce hanya.

ABUBUWAN DA ZAKU BUKATA SUNE KAMAR HAKA.

• Karas kamar 5.

• Lemon Tsami kamar 1.

• Tacaciyar Zuma kamar Cokali 4.

• Ruwa kamar Kofi 2.

YADDA ZAKU HADA.

Da farko zaku dauki karas dinku saiku kankare bayansa kadan, bayan ya kankaru saiku yayyankashi sala-sala ku ajiye a gefe.

Saiku dauki Lemon Tsami dinku ku matse ruwansa da kyau a wani kofi mai kyau.

Zaku kuna wuta saiku dora tukunyarku kuzuba ruwa kamar kofi biyu, ku kawo wannan Karas naku da kuka yanka sala-sala saiku zuba a cikin wannan tukunya mai ruwa kofi biyu, kudafashi sosai na wani dan lokaci.

Saiku sauke kusamu wani abu ku markada wannan Karas din bayan yayi sanyi kenan idan ya markadu zai koma kamar haka.

saiku ajiye a gefe saiku dauko Lemon Tsamin da kuka matse ku zuba a ciki hade da zuma dinku kamar cokali 4 saiku juya sosai yadda ya kamata.

Akarshe sai kusamu rariya kamar ta tace shayi kokuma wata daban saiku tace sosai a wani Kofi mai kyau, saiku sanya a firji yayi sanyi idan kuma buka saiku dinga sha a kullum.

ABIN LURA:

Wannan hadi da muka baku ba a iya wankin Hunhu ya tsaya ba yana magani kmar haka.

• Ciwon Gabobi.

• Kunburin Ciki.

• Zugi ko Radadin Ciwo.

• Kawar Da tsiko na tsoka.

• Kawar da gajiyar jiki.

Da dai sauransu fatan zaku gwada wannan hadi, Allah yaba da lafiya Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button