Magunguna

YADDA ZAKI GYARA NONUWANKI DA SUKA KWANTA

YADDA ZAKI GYARA NONUWANKI DA SUKA KWANTA CIKIN SAUKI.

Yaku yan uwana mata shi kwantaccen nono kansamuwa ta hanya iri daban daban wasu nonuwansu kan kwanta sakamakon shayarwa da suke wasu kuma nasu kan kwantawa ne saboda wani yanayi musanman yan matan dabasuyi aure ba.

To insha Allahu daga yanzu wannan magani zai dago miki da kwantaccen Nonanki yar uwa kedai ki nutsu kuma kiyi yadda akace.

ABUBUWAN DA ZAKI BUKATA A CIKIN WANNAN AIKI.

• Farar Shinkafa Ta Tuwo.

• Jar Masara.

• Alkam.

• Gero.

• Nono ko

• Yogot.

YADDA ZAKI HADA WADANNAN MAGUNGUNA.

Kisamu wadannan Farar shinkafa, Jar Masara, Alkam, Gero din nan naki saiki wanke su ki shanyasu su bushe saiki dan soyasu sama-sama sai a nika miki su, amma kuma zaki iya dakawa idan kina da karfin haka.

Saiki tankade bayan an nikasu kenan ko an daka, bayan kin tankade din saiki samu nono mai kyau ko kuma Yagot ta asali saiki debi wannan garin naki da kika tankade cokali daya da rabi ko biyu saiki dinga zubawa a wannan Nono naki ko yagot saiki juya sosai saiki shanye.

To yar uwa insha Allahu indai matsalar kwanciyar Nonuwanki ne to ta kawo karshe, yar uwa nonuwanki zasu dawo kamar na sabuwar budurwa, kuma zasuyi laushi da yaddar Allah .

Allah yabada ikonyi kuma a Turawa yan Uwa Mata don Suma su amfana.

ABIN LURA:

Amma Idan kinsan zakiyi yaye Kada kiyi, ki bari sai kinyi yayen kin gama warkewa daga cutar da ake fama da ita ta yaye , saikiyi kayanki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu