Magunguna

Yadda Zaku Rage Kiba Cikin Yan Kwanki Kadan

Assalam muna samun sakoninku dayawa kancewa wasu kiba na damun su sosai kuma har suna neman maganin dazasu mangance wannan kiba dake jikin su, domin sukansha wuya musanman da zafi

To insha Allah ka maganinsa hargida

ABUBUWAN BUKATA.

• Lemon Tsami 4 ko 5.

• Ruwa lita 2.

• Tukunya.

• Wutar Murhu, Rishoi ko Gas.

YADDA ZAKUYI

Ku wanke lemon tsamin ku sosai, saiku rabashi gida biyu biyu, saiku samu wani kofi ku matse ruwan lemon tsamin, bawan lemon tsamin kuwa saiku ajiyesu a gefe.

Saiku kunna wuta kota murhu ko risho ko kuma gas dinku, saiku dauko tunkunyarku ku dora a akan wutar saiku zubawa tunkunyar ruwa lita biyu mai kyau, saiku kawo wannan bawon lemon tsamin da kuka matse Ruwansa saiku zuba a cikin tunkunyar, zakuyi ta dafashu har na tsawon mintuna 30 ko 40 idan ma har yadahu zakuga launin fatar lemon  tsamin ya canza zuwa wata kalar.

Yadda zai koma idan yadahu

Idan kun tabbatar ya dahu saiki kashe wutar kokuma ku sauke ta a gefe saiku bari ruwan yayi sanyi sosai,

Idan kun tabbar yayi sanyi saiku debe wannan fatar lemon tsamin ta cikin tukunyar da kuka dafa, saikuma ku kawo wannan ruwan lemon tsamin da kuka matse a kofi saiku hadashi a cikin ruwan da kuka cire wannan fatar lemon tsamin maana wanda kuka dafa kenan.

Saiku juya sosai saiku sanya a firji don yayi sanyi idan kuma bakwa son sanyin sai ku barshi haka amma asamu wani abu mai murfi dazaa rufe saboda kura.

Zaa dinga shan ruwan kullum kofi daya sau hudu a rana. awa 1 kafin aci abinci. har tsawon kwanki shidda kokuma abin da ya sauwaka.

KARIN WASU AMFANIN LEMON TSAMI DA RUWAN DUMI A JIKIN MUTUM.

• Ruwan lemun tsami tare da ruwan dumi yana taimakawa wajen cin abinci da kuma tafiyar da jijiyoyin ruwa.

• Shan ruwan lemun tsami tare da ruwan dumi kowace safiya yana taimakawa wajen dai dai ta yanayin jiki.

• Shan ruwan lemun tsami tare da ruwan dumi shima yana taimakawa wajen rage ciwon gwiwa dana gabobi.

• Shan ruwan lemun tsami tare da ruwan dumi Yana taimaka wajen narkewar abinci.

• Shan ruwan lemun tsami tare da ruwan dumi Yana taimakawa wajen yaƙar cutar sanyi, mura dadai sauransu.

Yadda zai koma idan aka hadashi da wanda aka dafa da wanda aka matse

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu