Magunguna

Amfanin Sansami Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

Amfanin samsami ga dan adam nada yawa amma ga kaɗan daga cikin amfanin sa.

Don Magance fitsarin jini wato Tsargiya.
A samu saiwar Sansami da ganyensa da kuma sassaƙensa, sai a tafasa, a tace, a sa zuma, idan ya huce sai mai fama da fitsarin jini ya dinga sha.

Tana Maganin Cutar Kansa (cancer).
Ana hada saiwar Sansami da ganyensa da kuma sassaƙensa a jiƙa, sai mai lalurar ya dinga sha.

Tana Magance Zazzaɓi.
Mai fama da yawan Zazzaɓi, shi ma zai hada sassaƙen Sansami da saiwarsa da kuma ganyensa, ya dinga sha.

Tana Maganin Typhoid.
A tafasa ganyen Sansami da saiwarsa da sassaƙensa, a tafasa, sai mai fama da zazzaɓin typhoid ya dinga sha, da duminsa.

Tana Magance Ciwon mara Ga Mata.
Musamman ga mata, masu fama da ciwon mara, a tafasa ganyen Sansami da saiwarsa da kuma sassaƙensa, sai ta sa zuma, ta dinga sha, da duminsa.

Tana Magance Ciwon Basir.
Ana tafasa sassaƙen Sansami da saiwarsa da kuma ganyensa, idan ya huce sai mai fama da matsalar basir ya dinga sha.

Ga Masu Fama Da Fitsarin kwance.
Fitsarin kwance na manya ko na yara. A jika sassaƙen Sansami ko a tafasa, idan ya huce sai mai fama da fitsarin kwance ya dinga sha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu