Yadda Za’a Magance Ciwon Gwiwa
Daga cikin nau’o’in ciwon gwiwa da mutane ke fama da shi akwai ciwon gwiwa wanda a yaren kiwon lafiya ake cewa “Knee Osteoarthritis“, wannan ciwo ne da har a yanzu wasu mutane ke tunanin ciwon sanyi ne. Tabbas wannan ciwo ba shi da alaƙa da sanyi ko kaɗan.
Irin wannan ciwon gwiwa yana faruwa ne sakamakon ƙarancin ko sandarewar majinar gaɓa da ke tsakanin ƙasusuwan gwiwa, ko kuma zaizayewar gurunguntsi wanda shi ne matashin da ke tsakanin ƙashi da ƙashi wanda yau da gobe hakan zai sa ƙasusuwan gwiwar su ɗinga gugar juna.
Kasancewar gaɓar gwiwa gaɓa ce da ke ɗawainiyar dakon nauyin jiki tun daga kai har zuwa gwiwa a lokacin tsaiwa ko tafiya da kuma buƙatar motsawarta a mafi yawan lokuta, hakan ne yasa ciwon ke kama gwiwowin biyu dukka duk da cewa ciwon gwiwa ɗaya kan iya fin na ɗayar a lokaci guda.
Bincike ya nuna cewa wannan ciwon gwiwa na gaba-gaba a jerin larurorin da ke iya kassara ko ma durƙusar da mutane ɗungurungum a faɗin duniya. Saboda haka tasirin ciwon yana da babbar illa ga ingancin rayuwa, walwala da tattalin arziƙin masu fama da wannan ciwo.
ALAMOMIN CIWON GWIWA
Masu irin wannan ciwon gwiwa su kan fama da:
• Ciwo mai ɗabi’ar tsuko a cikin gwiwa musamman da daddare ko da safe.
Haka nan yau da gobe ciwon gwiwar kan haifar da canje-canje a gaɓar gwiwa kama daga ƙasusuwan, zuwa gurunguntsai, tantanai da tsokokin dake aiki akan gwiwar. Misali, raguwar tazarar da ke tsakanin ƙasusuwan gwiwa, ɗaurewar gungun tsokokin cinya na baya, da kuma raunin gungun tsokokin cinya na gaba, da dai sauransu.
Masu haɗarin kamuwa da irin wannan ciwon gwiwa sun haɗa da:
- aɗanda shekarunsu suka miƙa.
- Masu ƙiba.
- Masu haɗarin samun rauni ko bugu a gwiwa, musamman ga masu wasannin guje-guje da tsalle-tsalle.
- aɗanda sana’o’insu ke buƙatar ɗaukar nauyi da daɗewa a tsaye, da sauransu.
Kasancewar wannan ciwo yana faruwa ne yau da gobe, kaɗan da kaɗan, kuma yana da matakan ciwo da naƙasu hawa hawa.
• Kumburin gwiwar ƙaf.
• Riƙewar gwiwa.
• Idan ma ciwon ya ta’azzara akan ji sautin gugar ƙasusuwan ƙurus-ƙurus a yayin lanƙwasa ko miƙar da gwiwar ko kuma yayin tafiya.
MATAKAN CIWO KO NAƘASUN GWIWA
- Mataki na farko shi ne yake da mafi ƙarancin ciwo da naƙasu.
- Mataki na biyu kuwa shi ne matsaƙaicin ciwo da naƙasu.
- Sai mataki na uku shi ne lokacin da zaizayewar ta kai matuƙa kuma shi ne mafi tsananin ciwo da naƙasu.
Don haka samun sauƙin wannan ciwon gwiwa yana da alaƙa da ɗaukar matakan gaggawa tun da wuri domin fara shawo kan matsalar ciwon. Misali matakin farko na ciwon zai fi sauƙin magani akan mataki na uku.
Don haka wannan cibiya tamu ta Haske Islamic Medicine taga ya dace tabaku wata fa’ida dake dauke da sinadarin dake dawo da wannan sinadarai dake kawo zaizayar gwiwar wanda cikin abincinku ne na gargajiya da kuka watsar bakuson amfani dashi.
MAKANI::
Wannan abun dai ba komai bane illa makani wanda wasu sukan kirashi da walahan wasu kuma suna ce mashi Gwaza.
Nasan dai kowa yasan daya daga cikin wannan sunayen ko?
Yanda za’ayi da wannan makanin kuwa shine a same ta da bawon ta, sai adafa ta ta dahu sosai bayan ta dahu sai a bare adinga cinta kullum tsawon sati uku aga ikon Allah koda ka warke to yana da kyau adinga dafa maka ita lokaci zuwa lokaci kanaci kusani sinadaran dake bawon yafi na na makanin da kaso 60%.
Karin bayani akwai wasu abinci da kuke ferewa kafin ku dafasu daga yau kudaina feresu kafin kudafa su misali Doya da Dankali dashi makanin. Dukkansu bawonsu akwai waraka na cututtuka.