Magunguna

Amfanin Lemun Tsami Guda 6 Da Yakamata Kowacce Mace Ta Sani

Dukanmu mukan yi amfani da lemo sau da yawa, amma yawancin mu ba ma san ainihin Amfanin sa ba musanman ga mata. Ana iya amfani da lemon tsami a kicin, amma ba iya nan amfanin sa ke tsayawa ba. Kamar yadda wataƙila kun riga kuka sani, lemun tsami yana ɗauke da sinadaran bitamin B da C, da calcium, potassium, magnesium da phosphorus. Wanda suke da kyau ga lafiyar mu.

Lemun tsami na iya inganta jiki, magancewa da hana kamuwa da cuta, yana ƙarfafa tsarin garkuwar jikin mu har ma da rage yawan nauyi. Ana iya amfani da su ta hanyoyi daban-daban, amma a cikin rubutun yau, zan nuna muku yadda ake amfani da su don magance wasu matsalolin.

Anan akwai hanyoyi guda 6 na amfani da Lemon tsami wanda yakamata mace ta sani

YANA SANYA FATA TAYI KYAU DA LAUSHI

Shafa ruwan Lemon Tsami yayin kwanciyar bacci kansa ya fatar jikin ki tayi kyalli da laushi, da kuma kashe wasu kwayoyin cututtukan da ke a jikin fata.

YANA HASKAKA GASHIN KU. 

Kusamu ruwan Lemon tsami ku shafa a gashin kanku sauki barshi ya bushe zuwa wani dan lokaci sai a wanke da ruwan ɗumi, zai sanya gashin kanku kyalli kana yayi baki da tsawo kuma ya kashe muku ƙaiƙayin gashin kai.

YANA KAWAR DA TABO AKAN FATA. Sanya ruwan Lemon Tsami akan tabo dake jiki kan kawar da duk wani tabo dake jikin ki, kawai a samu auduga sai a dangwali ruwan Lemon Tsami a goga a inda tabon yake.

YANA HANA TSINGEWAR LEBBA.

Yanayin sanyi dake saka bushewar fata ko rashin wasu bitamin na iya haifar da tsagewar leɓuna. Ruwan lemun tsami na iya zama babban taimako idan kuna son kawar da wannan matsalar. Abin da kawai za ku yi shi ne a shafa ruwan lemun tsami kadan a lebe kafin kwanciya barci, zai samar da laushi sosai a labben ku.

ANA SANYA FARCE YAYI FARI SOSAI

Shafa ruwan Lemon Tsami a kan FARCE kansa ya FARCE yayi ƙarfi bazai dinga karye wa ba. Kwai ku samu auduga ku dinga gogawa a kan farcen yayin kwanciyar bacci.

HANA WARIN YAMMA TA:

Idan kuna fama da warin hammata shafa ruwan Lemon tsami a hammata zai kawar muku da warin hammata. Kawai zaku samu auduga sai ku dangwali ruwan Lemon Tsami sauki shafa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu