LabaraiSiyasa

Gwamnatin Kano Za Ta Fara Raba Abinci Kyauta Ga Yan Jihar

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yace babban bankin kasar nan CBN bai yi la’akari da makomar mutane ba gabanin aiwatar da sauyin kudi da yayi ba.

Ganduje na wannan jawabi ne a jiya Alhamis yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a dakin taro na Africa House dake fadar gwamnatin Kano, inda yace tsarin cike yake da kurakuren da ka iya durkusar da tattalin arzikin kasa da kuma kawo nakasu ga Demokaradiyya.

Yace bai Kamata CBN ya dauki irin wannan salo ba tare da samawa mutane mafita ba, wanda a cewar sa hakan ke alamta rashin kwarewa daga bangaren mahukuntan babban bankin.

Gwamnan ya kuma Kara da cewa gwamnatin Jihar nan zata Samar da motocin sufuri dogaye don ragewa mutane radadin halin da suka samu Kansu baya ga shirin raba kayan abinci ga daukacin kananan hukumomin jihar nan.

A cewar Gwamnan za a rabar da abincin ne ga mábukata da suka cancanta, a kokarin gwamnatin na ganin an saukakawa al’umma.

A nasa jawabin Madakin Bichi Isyaku Muhammad Tofa yayi Kira ga CBN da su lamincewa jama’a ci gaba da amfani tsofaffin kudin tare da sababbin kamar yadda ake Yi a kasashen da tattalin arzikin su ya habaka.

MANUNIYA ta rawaito cewa taron masu ruwa da tsakin ya samu halartar daukacin sarakunan Kano da wakilan bankuna da saura al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button