Siyasa

YANZU – YANZU: Tinubu ya bayyana yadda Najeriya za ta shawo kan kalubalen da ta ke fuskanta

Kalubalen dake addabar Najeriya sun fi karfin hadin kai, imani da jajircewa, in ji dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu.

Tinubu ya bayyana haka ne a taron Meet the Mentor Dinner da kungiyar Progressive Sisters Network (PSN) ta shirya ranar Lahadi a Abuja.

“A matsayinmu na kasa, muna fuskantar wasu kalubale, amma ana iya shawo kan wadannan kalubale. Muna da ikon nemo hanyarmu a cikin yanayin da kamar babu wata hanya.

Don Allah, mu yi aiki tare don gina Nijeriya ta burinmu. Na san abu ne mai wuya ba a nemi hanya mai sauki a Nijeriya ta yau ba, amma tare da imaninmu da juna da kuma al’ummarmu, za mu iya magance matsalolinmu,” in ji shi.

Tinubu ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasar, zai tabbatar da cewa an yi amfani da albarkatun ma’adinan Najeriya yadda ya kamata domin kawo mata daukaka.

“Za mu samu daukaka a kasar nan, mu yi imani da kanmu kawai,” in ji Tinubu ya kuma gode wa wadanda suka shirya liyafar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu