Labarai

Allah Sarki Abun Tausayi, Kalli Jerin Matasa 7 da Masu Kwacen Waya Suka Kashe a Kano Cikin Wata daya

Allah Sarki Abun Tausayi, Kalli Jerin Matasa 7 da Masu Kwacen Waya Suka Kashe a Kano Cikin Wata daya.

Allah Sarki Abun Tausayi, Kalli Jerin Matasa 7 da Masu Kwacen Waya Suka Kashe a Kano Cikin Wata daya

Kamar dai yadda aka sani acikin Kwanakin nan wata fitina ta Kunno kai ta masu kwacen wayoyin mutane Wanda dama akwai sai yanzu ne ta kara Dawowa inda har takaiga Yanzu bama Wayar kawai suke Kwacewa ba har kisa sukeyi.

Mutane da dama sunata kawowa jami’an tsaro korafi akan irin Abubuwan da suke faruwa acikin unguwanni na daga jahohin da suka hada da Kano, Katsina, Kaduna inda wannan sune jerin jahohinda Wannan bala’i ya addabi mutane da Wasu sauran jahohin.

Tun daga bayan karamar sallah izuwa Yanzu an samu jerin matasa guda kusan bakwai wanda aka hallaka a jahar kano Kawai bayan Wadanda aka yankewa hannuwa a wasu jahohin ta Hanyar masu kwacen waya.

Wannan dai ba Karamin abin takaici bane kasancewar akwai hukuma a dukkan jahohin nan da wannan bala’i ya addabi Mutane amma har yanzu babu wani mataki a bayyane da hukumomi suka dauka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu