Labarai

Yadda Wani Matashi Ɗan Najeriya Ya Damfari Wata Mata Maƙudan Kuɗaɗe a Indiya

Yadda Wani Matashi Ɗan Najeriya Ya Damfari Wata Mata Maƙudan Kuɗaɗe a Indiya.

Wani matashi ɗan Najeriya ya shiga hannun ƴan sanda a ƙasar Indiya bayan ya tafka wata katoɓara.

Matashin mai shekara 26 a duniya ya shiga hannu ne bayan ya damfari wata mata maƙudan kuɗaɗe har naira miliyan talatin da ɗaya bayan yayi mata alƙawarin aure.

Matashin mai suna Bernard Chukwunonsu, wanda yake zaune a Uttamnagar a birnin New Delhi, an cafke shi ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Janairun 2023. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Kwamishinan ƴan sanda na Surat, Ajay Kumar Tomar, ya bayyana cewa:

Wanda ake tuhumar ya ƙulla ƙawance da matar a kafar sada zumunta sannan yayi mata alƙawarin zai aure ta. Daga baya sai wanda ake tuhumar da abokinsa suka kirata a waya a matsayin ma’aikatan kula da shige da fice.”

Sun gaya mata cewa an kama saurayinta sannan an ƙwashe wata jakar kaya a hannun sa.”

Wanda ya kira wayar ya buƙaci da ta bayar da kuɗade domin a sako saurayinta tare da jakar. Matar ta tura kuɗi har Rs 57.39 lakh a asusun ajiya na banki na wanda ake tuhumar daga ranar 1 ga watan Disamba zuwa ranar 12 ga watan Disamba.”

Bayan wasu ƴan kwanaki kawai sai wanda ake tuhumar yayi ɓatan dabo ya daina ɗaukar kiranta a waya idan ta kira shi.”

Ƴan sanda sun shigar da laifi bisa sashin doka 419, 420 da 120b na dokar yanar gizo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu