Da dawowar Tinubu Rara ya kaimai kukan sa akan kona masa gidan da akayi
Wanda duk yake jima’i da matarsa baya jin dadi ko bai taba jin dadin saduwa ba yazo ga magani.
Ko kema kina mamakin miyasa baki jin dadin jima’i ko baki da sha’awa, sai ku duba ku gani mai yiwuwa wannan bayanai zasu iya baku haske akan matsalar dake damunku domin neman mafita.
Duk da yake anfi ganin cewa, mata sunfi maza yawan sha’awa da son jima’i a yanayin halittarsu akan maza, ba abin mamaki bane a sami akasin haka wani lokacin cewa akwai mata da yawa wanda basa da sha’awa ko kwadayin jima’i sabida wasu dalilai na lafiya.
Hakan na faruwa inda zaka sami mace na gudun kwanciyar aure ko bata damu da ayi kwanciyar ba ko kada ayi duk daya ne a gurinta, sabida koda anyi ma bata jin dadin jima’in sam-sam ko kuma bata jin dandanonsa irin yanda take tsammani ake ji, kamar yanda sauran mata ‘yan uwanta ke jin dadin rayuwar aure da mazajen su.
Tana yin kwanciyar aure ne kawai a matsayin wani aiki na biyan bukatar mijinta ba bukatar taba, kuma ba don tana jin dadi ko gamsuwa ba, sai dai kawai don bautar aure ko gudun fushin sabawa al’ada, ko kuma domin kare mijinta daga fadawa tarkon zina.
Hakika akwai mata da yawa da suke cikin wannan yanayin rayuwar aure marar dadi, wanda sun hakura da hakkinsu na jin dadin aure inda wasu matan kuma ke kokarin neman mafita daga wannan matsala ta neman hakkinsu daga mazajensu ko neman magani.