Siyasa

INEC ta dora kashi 88% na sakamakon zabe kwanaki 6 bayan zabe

INEC ta dora kashi 88% na sakamakon zabe kwanaki 6 bayan zabe

Ya zuwa yanzu dai hukumar zabe mai zaman kanta ta fitar da sakamakon zabe 155,472 daga rumfunan zabe 176,846, kwanaki shida bayan zaben shugaban kasa.

Adadin ya nuna kashi 88 cikin 100 na sakamakon da aka samu daga dukkan rumfunan zabe.
Har zuwa lokacin shigar da wannan rahoto, ana ci gaba da watsa sakamakon na’urar.

‘Yan Najeriya sun yi tsammanin za a dora sakamakon zaben a ranar zabe kamar yadda shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi alkawari.


Sai dai INEC ta sha suka kan gazawarta na saka sakamakon zabe a dandalinta na kallo wanda hakan ya sa wasu wakilan jam’iyyu suka fice a ranar Litinin a dakin taro na kasa da ke Abuja.


Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto a ranar Juma’a, har yanzu ba a shigar da sakamakon dukkan rumfunan zabe a shafin na INEC ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu