Kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi ta zama Jami’ar ilimi karkashin mulkin Ganduje
Kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi ta zama Jami’ar ilimi karkashin mulkin Ganduje
Hotunan yadda Shugaban hukumar kula da Jami’o’i ta Kasa Prof. Abubakar Adamu Rasheed yake mika takardar amincewa da maida Kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi jami’ar ilimi ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR.
kwalejin Sa’adatu Rimi ita ce kwaleji mai daraja ta biyu a cikin tsofaffin kwalejojin ilimi da ke Arewacin Najeriya baya ga tsohuwar kwalejin horar da malamai ta Kano, da a yanzu take jihar Jigawa, wato (Gumel Advance teachers’ College).
Wannan shaida ce ga irin jajircewar da Gwamna Ganduje yake yi wajen bunkasa harkar ilimi a Jihar Kano.
Tun a shekarar 2021 Gwamna Ganduje ya tabbatar da cewa shirye shirye sun yi nisa dan ɗaga darajar kwalejin ilmin zuwa matakin Jami’a.
Gwamna Ganduje ya cika wannan alkawari na daga darajar Kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi izuwa jami’ar ilimi a jiya Talata.
Abubakar Adamu Rasheed ya godewa Gwamna Ganduje tare da yaba masa bisa jajircewarsa dan ganin wannan kuduri ya tabbata.
Gwamnan ya samu rakiyar Mataimakinsa Dr Nasiru Yusuf Gawuna da sanata Barau Jibril da Kwamishiniyar Ilimi mai zurfi, Dr Mariya Mahmud Bunkure da Kwamishinan yada labarai, Comrade Muhammad Garba da shugaban jami’ar Sa’adatu Rimi, Prof.
Yahaya Bunkure da shugabannin manyan makarantun Kano da sauran jami’an Gwamnati.