Labarai

Sake fasalin Naira: AGF Malami wani makiyin jama’a – Onanuga.

Sake fasalin Naira: AGF Malami wani makiyin jama’a – Onanuga.

Daya daga cikin masu magana da yawun kungiyar Bola Tinubu, Kashim Shettima Presidential Campaign Council, Bayo Onanuga, ya bayyana Atoni Janar na Najeriya, Abubakar Malami, a matsayin makiyin jama’a.

Bayanin nasa na kunshe ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba.

Onanuga yace Malami ya bi sahun gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele.

“Abubakar Malami kuma makiyin jama’a ne kamar Emefiele,” ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya na mai da martani ne kan matakin farko da ministan shari’a ya shigar ta hannun lauyoyinsa Mahmud Magaji da Tijanni Gazali, inda ya bukaci kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar da wasu gwamnonin arewa uku suka shigar domin dakatar da aiwatar da manufar sake fasalin kudin Naira na CBN. AGF ta yi zargin cewa Kotun Koli ba ta da hurumin sauraron karar.

Ya kuma kara da cewa “masu gabatar da kara ba su nuna dalilin da ya dace na daukar matakin a kan wanda ake kara ba.”

Idan za a iya tunawa, gwamnonin Yahaya Bello na Kogi, Nasir El-Rufai na Kaduna da Bello Matawalle na Zamfara sun maka babban bankin kasa CBN da gwamnatin tarayya a gaban kotun koli inda suka bukaci a dakatar da aiwatar da manufofin sake fasalin naira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu