Shugaban Amurka Joe Biden, Ya yi Gargadin Cewa Amurka Za ta kare kanta Daga China Idan ana Barazana Ga Ikonta..
Za mu yi aiki idan China ta yi barazana ga ikon mallakarmu..
Shugaban Amurka Joe Biden, ya yi gargadin cewa Amurka za ta kare kanta daga China idan ana barazana ga ikonta.
Biden ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron hadin gwiwa a birnin Washington ranar Talata.
Shugaban na Amurka ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da Beijing idan manufofinta na tattalin arziki da siyasa sun dace da na gwamnatin Amurka da na duniya baki daya.
Sai dai ya kara da cewa kasarsa za ta kare ikonta daga duk wani ta’addanci daga China, kamar yadda CNN ta ruwaito a ranar Laraba.
“Na kuduri aniyar yin aiki tare da China inda za ta iya ciyar da muradun Amurka da kuma amfanar duniya,” in ji Biden.
Amma kada ku yi kuskure … idan kasar Sin ta yi barazana ga diyaucinmu, za mu dauki matakin kare kasarmu.
Kalaman na Biden a lokacin da yake jawabi a ranar Talata da daddare ya zo ne a daidai lokacin da takun-saka tsakanin Amurka da China ke kara ta’azzara bayan da ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta gano wani balon leken asiri na China da ke shawagi a sararin samaniyar Amurka, wanda aka harbo a tekun Atlantika.
Wannan ci gaban ya tilastawa sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken soke ziyarar da ya shirya zuwa China
Rahotanni sun ce a wannan na iya kawo rugujewar fatan da ake yi na rashin jituwa tsakanin Washington da Beijing bayan ganawar da Biden ya yi da shugaban kasar Sin Xi Jinping a watan Nuwamba na shekarar 2022