Magunguna

Hanya Ta Biyu Wajen Kawar Da Kurajen Fuska Ko Tabo A Jiki

Yan Uwa idan kuna biye damu a Darasin baya munyi muku bayani akan kurajen fuska da tabo a fuska ko jiki. Wanda wannan matsala kan kawo matsalolin rashin laushin fuska ko jiki.

Fuska ko Jiki kan bushe ne saka makon fitar wannan kuraje, haka zalika idan tabo ne jikin mutum kan kode wani wurin baki wani wurin fari.

Wannan dalili yasa muka kuma binciken wasu hanyoyi har guda Biyu don magance wannan matsalar.

Abubuwan Da Zaku Nema Shine;

  1. Lemon Tsami.
  2. Bawon Ayaba.
  3. Zuma.

Yadda Zakuyi Dasu;

Da farko zaku samu Lemon Tsaminku saiku yankashi biyu, ku ajiye a gefe. Saiku samu sabon Bawon Ayaba dinku ku yayyanka shi yadda ya kamata.

Kurajen fuska kurajen da kan fito a fuska, yawancin sukan fito suyi ruwa bayan ruwan kuma sai suyi tabo maana sai fuskar mutum tayi baki baki wanda hakan kasanya

Saiku samu bawon Ayaba dinku ku matsa ruwa lemon tsamin a kan Bawon Ayabar saiku kawo zuma shima ku zuba a kai.

Abin Lura:
Wannan hadi bawai iya kuraje ko tabo yake magani ba yana gyara fata tayi loushe, santsi, sheki da kuma kariya daga wasu cututtuka masu afkawa fata.

A turawa yan uwa da abokan arziki don suma su sani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button