Wasanni

QATAR 2022:- Ƙasar Senegal da Netherlands Za Su Gwada Kaimi Bayan Kaye Da Qatar Ta Sha A Hannun Ecuador

A ranar Lahadi aka bude gasar ta cin kofin duniya a Qatar, inda mai masaukin bakin ta sha kaye a hannun ‘yan wasan Ecuador da ci 2-0 a wasan farko da aka buga a gasar.

Kasar Netherlands za ta fafata da Senegal a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar.

Netherlands dai ba ta je gasar da aka yi a Rasha a 2018 ba, hakan ya sa ake ganin ta zo da zafinta a wannan karo.

Abu na farko da masu sharhi kan kwallon kafa suka bayyana shi ne, kasar za ta nuna kwarewarta a gasar tare da nuna cewa ita fa ba kanwar lasa ba ce a tsakanin manyan kasashe irinsu Brazil, Faransa da Argentina.

“Ina da kwarin gwiwa akan wannan tawagar ‘yan wasa, ina ga za mu iya lashe kofin na duniya.” Kocin Netherlands Louis van Gaal ya ce.

Wani abu kuma da ksar ta Netherlands za ta yi nuni da shi a filin wasa na Al Thumama da ke birnin Doha shi ne, yadda ake sukar kasar ta Qatar da ke karbar bakuncin gasar kan tsauraran dokokinta da kuma yadda take hakkin bil Adama.

Abu na biyu, kasar ta Dutch ita ce jagora a kamfen da ake yi na dabbaka dabi’ar nuna kauna ba tare da nuna wariya ba karkashin shirin nan na “One Love.”

Ana kuma sa ran kyaftin din kungiyar Virgil van Dijk zai saka kambun hannun na kyaftin mai dauke da launuka, matakin da ya yi biris da kiran da FIFA ta yi na kada a saka siyasa a harkar gasar ta cin kofin duniya.

Senegal ana ta bangare, za ta kara a wasan ne ba tare da Sadio Mane ba, wanda aka ayyana a ranar Alhamis cewa yana fama da jinya a kafarsa ta dama.

Mane ya samu rauni ne a gasar Bundesliga ta Jamus a lokacin da kungiyarsa ta Bayern Munich take karawa da Bremen.

Hakan kuma babban gibi ne ga tawagar ta Senegal

“Wannan babban abin alhini ga Sadio Mane da tawagarmu. Kuma hakan babban kalubale ne a gare mu. Amma duk da haka, muna da tawaga kwakkwara.” In ji Kocin Senegal Aliou Cisse.

Sauran wasannin da za a buga a ranar Litinin sun hada da Ingila da Iran sai Amurka da Wales.

A jiya Lahadi aka bude gasar ta cin kofin duniya a Qatar, inda mai masaukin bakin ta sha kaye a hannun ‘yan wasan Ecuador da ci 2-0 a wasan farko da aka buga a gasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button