Wasanni

Coutois Da Benzema Ba Za Su Samu Buga Wa Real Madrid Club World Cup Ba

Coutois Da Benzema Ba Za Su Samu Buga Wa Real Madrid Club World Cup Ba.

Karim Benzema da Thibaut Courtois ba za su buga wa Real Madrid Club World Cup da Morocco ke karbar bakunci ba.

Ranar Laraba, Real Madrid za ta fafata da Al Ahly a wasan daf da karshe a gasar cin kofin duniya ta zakarun nahiyoyi.

Real din ta je Morocco ranar Litinin tare da ‘yan wasa 22, yayin da Eder Militao da Ferland Mendy da Eden Hazard da kuma Lucas Vazquez ke jinya.

Benzema, wanda ya lashe Ballon d’Or, ya ji rauni a wasan La Liga da Real ta ci Valencia ranar Alhamis.

Shi kuwa Coutois ya yi rauni a ranar Lahadi a wasan da Mallaorca ta ci Real Madrid 1-0.

An sauya mai tsaron ragar tawagar Belgium a wasan, inda dan kasar Ukraine, Andriy Lunin ya maye gurbinsa.

Rashin nasarar da Real ta yi ranar Lahadi ya sa Barcelona wadda ta doke Sevilla 3-0 ta ba ta tazarar maki takwas, bayan kammala wasannin mako na 20.

Real na fama da ‘yan wasan da ke jinya a kakar nan, bayan da David Alaba da Aurelien Tchouameni suka koma atisaye.

Yan wasan da Real ta je da su Morocco buga Club World Cup

Masu tsaron raga: Lunin, Luis López da Cañizares.

Masu tsaron baya: Carvajal, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Rüdiger da Marvel.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, D. Ceballos, Mario Martín da Arribas.

Masu cin kwallaye: Asensio, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu