Wasanni

Barcelona ce kan Gaba a Manyan Gasar Zakarun Turai da ba a ci ta kwallaye Masu Yawa a lik ba.

Barcelona ce kan Gaba a Manyan Gasar Zakarun Turai da ba a ci ta kwallaye Masu Yawa a lik ba.

Barcelona ce kan gaba a matakin wanda aka ci karancin kwallaye a tsakanin manyan gasar Turai biyar a kakar nan.

Kawo yanzu kwallo bakwai ne ya shiga ragar Barcelona a La Liga, bayan wasa 20 da aka yi a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Wannan kwazon ya sa Barcelona, wadda ke jan ragamar teburin La Liga ta bai wa Real Madrid tazarar maki takwas, wadda ke biye da ita.

Haka kuma Barca ta yi wasa 15 a dukkan fafatawa a bana ba a doke ta ba, wadda ta dauki Spanish Super Cup a Saudi Arabia cikin watan Janairu.

Kungiyar ta Nou Camp ta kai zagayen daf da karshe a Copa del Rey, za kuma ta yi gumurzu da Real Madrid a wasan hamayya na El Clasico.

Kungiya ta biyu a Turai da ba a ci ta kwallaye da yawa a Turai ba, ita ce Newcastle United, wadda 12 suka shiga ragarta kawo yanzu.

An ci Real Madrid kwallo 17 a La Ligar kakar nan, Atletico Madrid ma 17 aka zura mata a raga da Real Sociedad da kwallo 19 ya shiga ragarta.

Bayan wasa 20 a La Liga, Barcelona ta ci kwallo 42, Real Madrid kuwa 40 ta zura a raga kawo yanzu.

Ranar Lahadi 12 ga watan Fabrairu, Barcelona za ta ziyarci Villareal a wasan mako na 21 a gasar La Liga.

Real Madrid wadda za ta kara da Al Hilal a wasan karshe a Club World Cup a Morocco ranar Asabar, za ta buga La Liga da Elche ranar Laraba 15 ga watan Fabrairu a Santiago bernabeu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu