Wasanni

Champions League: Messi ba zai buga karawar PSG da Bayern Munich ba

Dan wasan gaba na Paris Saint-Germain, Lionel Messi yana shakkar buga wasan farko na gasar cin kofin zakarun Turai karo na 16 da Bayern Munich saboda matsalar kafarsa, in ji L’Equipe.

Messi ya buga minti 90 na wasan da suka sha kashi a hannun Marseille da ci 2-1 a gasar cin kofin Faransa ranar Laraba.

Duk da haka, daga baya ya ji zafi a hammatar sa.

Ana sa ran Messi ba zai buga wasan da PSG za ta yi da AS Monaco a gasar Ligue 1 ranar Asabar, kwanaki uku kafin wasan Bayern.

Messi ya ci wa PSG kwallaye 15 a wasanni 25 da ya buga a gasar ta bana.

Zakarun Faransa tuni ba su da dan wasan gaba Kylian Mbappe a wasan bayan da ya samu rauni a cinyarsa a makon da ya gabata.

Za a yi wasa na biyu a Munich ranar 8 ga Maris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu