Real Madrid Ta Kara Lashe Fifa Club World Cup
Real Madrid Ta Kara Lashe Fifa Club World Cup.
Real Madrid ta doke Al Hilal 5-3 ta lashe Fifa Club World ta dauki na biyar na takwas jimilla har da na sauya fasalin gasar.
Morocco ce ta karbi bakuncin gasar kofin duniya ta zakarun nahiyoyi da aka kammala ranar Asabar.
Real Madrid ta ci kwallayen ta hannun Karim Benzema da Federico Valverde da ya ci biyu da Vinicius Junior da shima ya zura biyu a raga.
Al Hilal kuwa ta ci nata kwallayen ta hannun Moussa Marega da kuma Luciano Vietto da ya zura biyu a raga.
Kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama ta lashe kofi hudu daga tsakanin 2014 zuwa 2018, sannan ta kara da na 2023.
Real Madrid mai rike da Champions League ta kai wasan karshe, bayan doke Al Ahly ta Masar 4-1 a karawar daf da karshe ranar Laraba.
Al Hilal mai rike kofin zakarun Asia ta kai wannan matakin bayan cin Flamengo 3-2 ranar Talata – ta zama ta farko daga Saudia da ta buga wasan karshe a gasar.
Flamengo ta Brazil ce ta zama ta uku a wasannnin da aka yi a Morocco, bayan doke Al Ahly ta Masar 4-2 ranar Asabar.
Fifa ta tsara yadda za ta sauya fasalin gasar Club World Cup daga Yunin 2025, inda kasashe 32 za suke karawa duk bayan shekara hudu.