Tattaunawa Da Ibrahim Mandawari Akan Rayuwar Sa Da Baku Sani Ba. Nina fara yin Producer A Kannywood 1990
ME NE SUNAN KA ?
Ni sunana Ibrahim Muhammad Mandawari.
HAR YANZU KANA FIM KO KA DAINA ?
Aa, har yanzu ina fim.
SHEKARUN KA NAWA A KANNYWOOD ?
Dayake ina daga cikin wadanda muka kirkiro wannan masana’anta to kaga adadin shekarun ta adadin, zamana a ciki.
Ita KANNYWOOD An budeta tin 1990 a watan Maris wanda kuma nine producer na farko.
TO A HARKAR FINA-FINAI BAKI DAYA FA ?
1990 Wasu mutane suka bamu Kwarin giwwa.
KO ZAKA IYA ANBATO SUNAN WASU DAGA CIKINSU ?
Akwai Emirates professor Dan Datti Abdul-Kadir, Alh-Mudi Speaking,
Doctor J N A Hamza, Mai Martaba Sarkin Kano Alh-Dr Ado Bayero.
WANE FIM DINKA KAFI SO ?
Jamila/Jamilu.
YAN MATA SUNYI MUKU RUBUBI LOKACIN DA KUKE SAMARI ?
Kasan ita harkar fim harka ce ta sha’awa kuma baka raba mace mai karancin shekaru da sha’awa.
Sabo da haka wannan ba sabon abu bane.
YA KA RIKA FAMA DA SU A LOKACIN ?
Hakuri muka dinga yi.
A INA KUKA HADU DA MATARKA ?
Matata Zohuwar magana ce saboda iyayen mu ne mata suka hada abun Allah ya tabbatar dashi.
BAYAN NAN KA SAKE WANI AUREN ?
Ehh, ina da mace ta biyu.
KANA SHIRIN KARAWA NAN GABA ?
Toh, Allah Masani.
WANE ABINCI KA FI SO ?
Koko da Kosai.
WANE IRIN NAMA KAFI SO ?
Ehh, gaskiya nafi amfani da naman Saniya.
AKWAI WANI ABU DA KAKE NADAMAR YIN SA ?
Ehh, akwaii fim Wanda matar mahaifina bata taba ganina a cikin shiri ba sai wannan kuma nayi abu a ciki Wanda nayi nadamar hakan.
WACE TAMBAYA A KA FI YIMAKA ?
Ya Danganta dashi mai kallon wani zaice kun fito da wance mai yasa baza kuyi aure ba.
WACE RAWA KAFI SON TAKAWA A FIM ?
Ni gaskiya nafison nafito a mai kwatar ”yanci ko nawa ko nawani.
MENENE BABBAN BURINKA A RAYUWA ?
Alhamdulillah Bai Wuce cikawa da imani ba gaskiya.
KASASHE NAWA KA JE ?
Babu yawa da FARKO naje Niger,Cameroon,Saudi Arabia,Dubai,India su kenan.
DA WA KA FI SO A HADA KU A FIM ?
Marigayiya Hauwa Dodo,Hauwa Maina.