Labarai

Hanyoyin da Za Ku Bi Don Rabuwa da Tsoffin Kuɗaɗen Ku, Ku Sami Sabbi.

Hanyoyin da Za Ku Bi Don Rabuwa da Tsoffin Kuɗaɗen Ku, Ku Sami Sabbi.

Najeriya Yayin da wa’adin CBN ke kara gabatowa, ‘yan Najeriya na ci gaba da nuna damuwa game da halin da za su shiga kan samun sabbin kudi.

Hakazalika, wasu da dama na kokawa kan halin da bankuna ke jefa mutane na karancin kudade da kuma dogayen layuka da ake samu a bankuna.

1- Za ku iya kai kudadenku banki, a ajiye ko a baku madadinsu .

Duk mai rike da tsohon kudi zai iya amfani da bankin da ke kusa wajen sanya kudadensa a asusu kafin cikar wa’adin CBN.

Duk da haka, ‘yan Najeriya na ci gaba da kokawa game da adadin kudin da za a iya bayarwa a banki ba.

A ka’idar da banki ta ta sanyam mutum ba zai iya karbar sama da N20,000 a kan kanta. Duk da haka, wannan hanyar dai ita ce hanya mafi sauki.

2- ATM zai iya ba ka kudin da ka ajiye a banki.

A bangare guda kuma, akwai ATM, domin ana iya cire adadi mai yawa da ya haura N20,000 a injunan ATM a fadin kasar nan.

Abin da ya tabbata daga CBN dai shine, babu wariya babu raini, kowa zai iya kai kudinsa banki domin a ajiye masa a cikin asusu. Mafi yawancin inda ‘yan Najeriya ke kokawa shine; su kawo tulin kudi tare da tsammanin a basu adadin da suka kawo a matsayin musaya.

Idan baku manta ba, an ba kowane dan Najeriya damar cire kudin da ya kai N500,000 a duk mako, kamfanoni kuma za su iya cire kudin da bai haura N5,000,000 ba.

3- Wakilin CBN za su bude muku asusu, ko su zuba muku kudadenku a bankinku.

CBN ya ce ya kirkiri shirin musaya domin rage wahala ga mutanen da ke nesa ga bankuna wajen mayar da tsoffin kudade banki.

A ranar 23 ga watan Janairu ne CBN ya ce yana da agent-agent da ke a fadin kasar nan da ke kan aiki shigar da kudaden ‘yan Najeriya banki.

Tsarin agent-agent na CBN zai taimakawa mutanen kauye wajen shigar da kudadensu cikin sauki tare da rage bin dogayen layuka a bankuna.

Irin wakilan na CBN sun hada kamfanonin POS da masu hada-hadar kudade da walet-walet da dama da ake amfani dasu a fadin kasar.

Ta wannan tsarin, yana da matukar sauki ga mutumin kauye ya mallaki asusun banki tare da ci gaba da zuba kudi ko don gaba. Dama CBN ya ce duk wanda aka ba tsohon kudi a banki to kada ya karba saboda hakan ya saba ka’idar da ake tafiya a kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button