Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Ummi Rahab

Rahab Salim wacce aka fi sani da Ummi Rahab (an haifeta a ranar 7 ga watan Afrilun shekara ta 2004) a garin Kaduna.[1] ‘Yar wasan kwaikwayo ce ta Kannywood[2] ‘yar rawa kuma ‘yar talla wacce tayi aure da mawakin Hausa Lilin Baba.

Farkon Rayuwa

An haifi Ummi Rahab a ranar 7 ga watan Afrilun shekarar ta 2004 a cikin garin Kaduna dake Arewa maso yammacin Najeriya.

Karatu

Ummi rahab tayi karatun firamare da sakandire a jihar kaduna, kafin daga baya ta koma garin Kano domin ci gaba da rayuwar ta.

Sana’a

Ummi Rahab na daga cikin jaruman Kannywood da suka fara taka rawa a wasan kwaikwayo tun suna ƙanana. Ummi Rahab ta fara fitowa a fim tun lokacin tana makarantar firmare tare da fim din da tayi fice da shi wato “Takwara Ummi”. A lokacin tana da shekaru goma a duniya inda ta fito a matsayin diyar Adam A Zango.

Ummi Rahab tayi fice a masana’antar fim na Kannywood kuma ta fito a bidiyon waƙoƙin Hausa da dama da suka hada da: Meleri – WUFF Dake.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Dana Ka Sauke Wakar