Labarai

Yadda mutane suke mutuwa a wajan haƙo zinare a Bauchi

Yadda mutane suke mutuwa a wajan haƙo zinare a Bauchi.

GA CIKAKKEN BIDIYON A NAN ƘASA 👇👇👇

Innalillahi Wainna ilaihirrajiun Matashi Dan Shekara 22 Ya Kashe Mahaifiyar sa yar Shekara 50 ta Hanyar Caka mata Wuka a jahar kano.

Wallahi ina cin karo da wannan labarin sai da kaina ya buga, take kaina ya fara ciwo, bansan lokaci da hawaye ya cika idona ba.

Subhanallah, wannan wani kalar zamani Allah ya kawo mu, ace uwa wacce ta silar zuwan ka duniya, ta dauki cikin ka wata tara cikin laulayi, yau lafiya ko babu lafiya har tsawon wannan lokaci, tazo ta haife ka bata daina hidima dakai ba, ta raine ka ta maka komai na rayuwa waiyazubillah

Ta sadaukar da lokacin ta, lafiyar ta, dukiyar ta duk Dan ta inganta rayuwar ka, har zuwa girman ka, amma yau ace kai silar barin ta duniya, wannan rayuwa dame tayi kama.

Wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba wannan aikin shaye shaye ne da muamula da miyagun kwayoyi, mahaifiya itace mace mafi daraja da ko wani da zaiyi alfahari da ita, yayi burin kyautata mata domin samun karshe mai kyau, wasu sun rasa ta tun basu San Kan su ba, suna kukan rashin ta a ko da yaushe, wasu da su taso da nasu suna burin kyautata musu domin samun karshe mai kyau.

Amma kai ka rasa dame zaka saka mata sai irin wannan mummunan sakayya.

Allah ka jikan wannan baiwa taka
Allah ka shiryar mana da zuri’a ka azurta mu da yaya masu albarka masu tausayin mu, iyayen mu kuma Allah ka bamu ikon yi musu biyayya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu