Siyasa

Rufa’i Sani Hanga Na NNPP Ya Lashe Zaɓen Sanatan Kano Ta Tsakiya – Yanzu

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Rufai Sani Hanga na Jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lshe zaben dan Sanatan Shiyya tsakiya ta Jihar Kano.

Da yake sanar da sakamakon, jami’in tattara sakamakon zaben, ya ce Sen. Rufai Sani Hanga na jam’iyar NNPP ya samu nasara ne da kuri’u 456,787 yayin da Abdulsalam Abdulkarim Zaura ( AA Zaura ) na jam’iyyar APC, wanda shi ne ke kan kujerar ya zo na biyu da kuri’u 168,677.

Kazalika jam’iyyar PDP ita ce ta uku Jam’iyyar ta zo da kuri’u 55,237.

Ya sanar da haka ne jim kadan bayan kammala tattara zaben dan Majalisar Dattawa a ofishin INEC da ke Kano.

Ku Cigaba Da Bibiyar Wannan Shafi Namu Mai Albarka na MANUNIYA.COM don cigaba da samun sabbin labarai cikin harshen Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu